A lardin Yunnan da ke a kudancin kasar Sin, akwai wani tsohon birni mai suna Dali wanda yau da shekaru sama da 600 ke nan da gina shi. Ko da yake an dade da gina wannan birni, amma ya zuwa yanzu dai tsarin tsohon birnin yana nan yadda yake.
Tsohon birnin Dali yana yammacin lardin Yunnan na kasar Sin, fadinsa ya kai murabba'in kilomita kimanin 6. Da an hangi birnin nan daga wani dutse da ke dab da birnin, za a ga tituna shimfide layi-layi kamar layukan gidan dara, kuma ga tsoffafin kofofi masu kayatarwa a tsattsaye. Idan ka shiga cikin birnin ta kofar, to, za ka tarar da tsoffin gidaje irin na gargajiya.
1 2 3
|