Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-01-16 17:23:03    
Yadda aka yi rigakafin ciwace-ciwacen da dabbobin gida suka kawo

cri

Mr. Wang ya kara da cewa, ciwace-ciwacen da dan Adam suka kamu da su tare sun kawo wa lafiyar dan Adam babbar barazana. A wasu kasashen kudu maso gabashin Asiya, mutane sun kamu da cutar murar tsuntsaye, wasu kuma har sun rasa rayukansu.

Wani mai bincike daban na wannan cibiya Shang Deqiu ya yi bayani cewa, akwai hanyoyi guda 4 da dabbobin gida suka yada ciwace-ciwace ga mutane, ya ce, 'hanyoyin da ciwace-ciwace suka yadu daga dabbobin gida zuwa mutane sun nuna bambam da juna, su kan yadu ta hanyoyin numfashi da hanyoyin narke abinci da kuma fata na dan Adam, ban da wannan kuma, mutane su kan kamu da ciwo saboda kwari sun tsotsa jininsu.'

Dazu nan mun gabatar muku da ciwace-ciwacen da mai yiwuwa ne dabbobin gida suka yada su ga mutane, saboda haka, tilas ne mu fi mai da hankulammu kan kiwon dabbobin gida. Amma a zahiri kuma, masu kiwon dabbobin gida da yawa ba su san yadda za su kiyaye kansu sosai ba. Madam Guo ta yi shekaru da dama tana kiwon wani kare a gida, hanyar kurum da ta kiyaye kanta ita ce wanke karenta da kumfar wanki.

Amma wanki ba ya iya warware dukan matsaloli ba. Masana sun yi nuni da cewa, da fari, wajibi ne a mai da hankali kan tsabta na dabbobin gida da aka kiwo, ban da wanki kuma, ya kamata a kan zolaya gashinsu kullum, a kan kashe kwayoyin cuta a gidajensu kullum, a kan share kashinsu cikin lokaci; na biyu kuma, masu kiwo su kan dubbuba halin da dabbobin gida suke ciki da kuma gashinsu, ko suka ci abinci yadda ya kamata ko a'a. Masana sun ba da shawara cewa, idan ana shakkar dabbobin da ya kiwo ya kamu da ciwo, to, nan da nan a kai su asibitocin dabbobi.

Sa'an nan kuma, lura da tsabta na mutum yana da muhimmanci sosai. Mr. Wang Chengxin ya kara yin bayani a kan wannan fanni da cewa, 'ina tsammani da farko tilas ne a lura da tsabta na kansa da na gidansa; daga baya, kada a taba dabbobin gida kullum, alal misali, kada a yi barci da su, na uku kuma, mutane sun iya yin allurar rigakafi.'


1  2