Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-01-16 17:23:03    
Yadda aka yi rigakafin ciwace-ciwacen da dabbobin gida suka kawo

cri

Yanzu mutane suna son kiwon dabbobi a gidajensu, wadanda suka hada da kyanwoyi da karnuka da dai sauransu. Amma tare da jin dadin kiwon dabbobin gida, kada mutane su manta da barazanar da wadannan dabbobi suka kawo musu. Mene ne ciwace-ciwacen da dabbobin gida suka kawo mana, yadda irin wadannan ciwace-ciwace suka yadu, kuma yadda mutane suka yi rigakafinsu? A cikin shirimmu na yau, mun yi magana kan wannan fanni.

Mr. Qin Liang mai shekaru 60 da haihuwa da wuya ne ya yi numfashi lami lafiya a kwanan baya, bayan da aka yi masa bincike a asibiti, an gano cewa, huhursa ya gamu da matsala, bayan da aka zurfafa binciken jininsa, a karshe dai an gane cewa, akun da Mr. Qin ya kiwo ya kawo masa matsalar huhu. Fikafikan akun sun kan dauki kwayoyin cuta, lokacin da yake tashi, ya zuba wadannan kwayoyin cuta cikin iska, ta haka Mr. Qin ya yi numfashin kwayoyin cuta da suka haddasa ciwon huhunsa.

Ban da Mr. Qin kuma, akwai mutane masu yawa da suka je asibitoci saboda ciwace-ciwacen da dabbobin gidansu suka kawo musu. Bisa abubuwan da aka yi bayani, an ce, ya kasance da ciwace-ciwace fiye da dari da dan Adam ya kan kamu da su a sakamakon kiwon dabbabi a gida, kamarsu haukan kare da zazzabin aku da dai sauran iri guda 20 ko fi.

Mai bincike na cibiyar sarrafa da rigakafin ciwace-ciwace ta kasar Sin Wang Chengxin ya ba da karin haske cewa, 'a ganin likitoci, mutane da dabbobin gida su kan kamu da ciwace-ciwace bai daya, da farko ciwace-ciwacen su kan yadu tsakanin dabbobi, daga baya mutane sun kamu da su a sakamakon kwayoyin cuta da dabbobin gida suka dauka.'

1  2