Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-28 16:05:44    
WHO ta shawarci manoman kasar Sin da su kyautata hanyar da suke bi wajen kiwon tsuntsayen gida

cri

Daga baya Mr. Shigeru Omi ya ba da shawara ga manoma da su ajiye tsuntsaye a kebance inda akwai iska mai kyau, kada tsuntsayen gida su yi bulaguro a lambuna cikin 'yanci, sa'an nan kuma kada yara su yi wasa da tsuntsayen gida, bayan da aka taba gashin kaji da kwansu, sai a wanke hannu cikin lokaci.

A sa'i daya kuma, manoma za su mai da hankali kan halin da tsuntsayen gida suke ciki, idan sun gano mutuwa ba ta daidai ba, tilas ne a kai wa hukumar shawo kan cututtuka masu yaduwa rahoto nan da nan, kada su kashe da sayar da kuma cin tsuntsayen da suka kamu da ciwo ko kuma suka mutu a sakamakon ciwo da kansu.

A gun taro na karo na 4 da ofishin kula da shawo kan mumunar annobar murar tsuntsaye na kasar Sin ya shirya a wannan wata, mataimakin firaministan kasar Hui Liangyu ya yi bayani cewa, daya daga cikin ayyukan shawo kan irin wannan annoba shi ne sa kaimi kan kyautata hanyar kiwon tsuntsayen gida. Ban da wannan kuma gwamnatin kasar ta sanar da yi wa dukan tsuntsayen gida na kasar allurar rigakafi. Mataimakin shugaban sashen likitocin dabbobi na ma'aikatar aikin noma na kasar Mr. Li Changyou ya bayyana a makon jiya cewa, tun daga watan Oktoba har zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta yi wa tsuntsayen gida fiye da biliyan 5 allurar rigakafi, yawan tsuntsayen gida da aka yi musu allurar rigakafi ya kai kashi 85 bisa dari ko fiye.


1  2  3