Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-28 16:05:44    
WHO ta shawarci manoman kasar Sin da su kyautata hanyar da suke bi wajen kiwon tsuntsayen gida

cri
Darektan sashen tekun Pacific na yamma na Kungiyar Kiwon Lafiya ta Kasa da Kasa wato WHO Mr. Shigeru Omi ya bayyana a ran 26 ga wata cewa, kasar Sin kasa ce da ta fi ajiye tsuntsayen gida masu yawa a duk duniya, babban matakin da ya kamata ta dauka don hana annobar murar tsuntsaye ta yadu tsakanin tsuntsaye da kuma dan Adam shi ne kyautata hanyar da manoman kasar Sin suke bi a fannin ajiye tsuntsayen gida.

Lokacin da yake zantawa da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua, Mr. Shigeru Omi ya bayyana cewa, ya kamata a kyautata halin da ake ciki a fannin kiwon tsuntsayen gida da kuma rage tuntubar da ke tsakanin dan Adam da tsuntsayen gida cikin dogon lokaci don shawo kan annobar murar tsuntsaye.

Kasar Sin kasa ce mai girma da take kiwon tsuntsayen gida, yawan tsuntsayen gida da mutanen kasar Sin suke kiwo ya kai biliyan 14.2. mutane masu yawa suna ajiye tsuntsayen gida a cikin lambunansu, har ma a cikin dakunansu a kauyukan kasar. Mutane suna cudanya da tsuntsayen gida sosai.

Mr. Shigeru Omi ya kara da cewa, bisa nazarin da aka yi wa dukan mutanen da suka kamu da annobar murar tsuntsaye a duk fadin duniya a yanzu, dukan wadannan mutane sun taba cudanya da tsuntsaye gida, kwayoyin wannan annoba sun kama dan Adam ne ta wannan hanya. Ko da yake haka ne, amma ba za a iya kashe dukan tsuntsayen gida don hana annobar ta kama mutane ba, shi ya sa ba yadda za a yi, sai a yi kokarin raba mutane da tsuntsayen gida. Idan an rage cudanyar da ke tsakanin mutane da tsuntsayen gida, za a rage damar kamuwa da annobar murar tsuntsaye. Amma ba za a canja hanyar gargajiya ta kiwon tsuntsayen gida cikin wani dare daya kawai ba, sai dai za a aiwatar da shi cikin dogon lokaci.


1  2  3