Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-22 11:39:53    
Jerin bala'i daga indallahi ya yi wa dan Adan gamgami

cri

A gaban bala'i masu tsanani, 'yan Adam su ma sun fara daukar matakai don kiyaye muhallin rayuwarsu. A karshen shekara ta 2005, wakilai sama da dubu 10 daga kasashe kusan 190 sun yi taro a birnin Montreal na kasar Canada, don halartar taro na karo na 11 na bangarori masu daddale tsarin yarjejeniyar sauye-sauyen yanayin duniya na MDD, don ba da shawara a kan yadda 'yan Adam za su fuskanci sauye-sauyen yanayi a karni na 21. Bisa shawarwarin da aka yi, an sami dan ci gaba a gun taron, amma a matsayinta na kasar da ta fi fitar da iska mai dumama yanayi a duniya, Amurka ta ci gaba da kin yin hadin gwiwa.

Wani masanin ilmin muhalli na jami'ar kimiyya da fasaha ta kasar Birtaniya, ya bayyana cewa, dole ne 'yan Adam sun kara kokari don kyautata muhallinsu. Ya ce, 'yarjejeniyar Kyoto' mataki ne na farko ko wasu matakai ne kawai da aka dauka. Idan muna son kyautata muhallinmu zuwa wani matsayi mai kyau kamar yadda ya kamata, kamata ya yi mu kara karfin yarjejeniyar da ninki 20. ko a yanzu ma, ana fuskantar matsaloli da dama a wajen aiwatar da yarjejeniyar da muka kulla, dole ne mu kara yin kokari.'

Masana sun nuna cewa, yin amfani da kimiyya a wajen kafa tsarin magance bala'i da kuma rage su a duk fadin duniya, zai ba da taimako ga dan Adam wajen fuskantar wadannan miyagun bala'i daga indallahi. A sa'i daya kuma, kiyaye muhallinmu kamar yadda ya kamata hanya ce mafi kyau wajen daidaita matsalar, haka kuma hanya ce da ya kamata kasa da kasa su bi tare.(Lubabatu Lei)


1  2