Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-22 11:39:53    
Jerin bala'i daga indallahi ya yi wa dan Adan gamgami

cri

A halin yanzu dai, mun kusan kawo karshen shekarar 2005, amma rahoton da kungiyar kula da yanayi ta duniya ta bayar dangane da sauye-sauyen yanayin duniya a shekara ta 2005 ya jawo damuwar mutane sosai. Bisa rahoton, ba dai kawai shekara ta 2005 ta kasance a matsayi na biyu a wajen zafin yanayi ba, har ma fari da ambaliyar ruwa da tsunami da dai sauran miyagun yanayi sun kara yin tsanani. Wadannan miyagun bala'i daga indallahi sun kawo hasarar tattalin arziki ga kasashe da shiyyoyin da bala'in ya shafa, haka kuma sun bakanta wa mazauna wurin rai. Muhalli tana yi wa 'yan Adam gamgami dangane da ayyukansu na yi amfani da albarkatun kasa ba kamar yadda ya kamata ba.

Da kyar a manta da girgizar kasa da tsunami na tekun Indiya da aka samu a farkon shekarar da muke ciki. Mutane kimanin dubu 75 sun gamu da ajalinsu a wannan mugun bala'in da ya faru ba zato ba tsamani. Daga bisani, a lokacin guguwar iska mai karfi na tekun Atlantic na tsawon rabin shekara, ko yawan iskar ko karfinta duka sun kai matsayi mai tsanani a tarihin dan Adam. A cikin muguwar girgizar kasa da aka samu a kudancin Asiya a watan Oktoba da ya gabata, mutane sama da dubu 80 sun riga mu gidan gaskiya, kuma ta zama daya daga cikin girgizar kasa da ta fi haddasa mutuwar mutane a shekaru 100 da suka wuce. Yanzu an kawo karshen shekarar, amma ga shi hadarin dusar kankara da iska mai sanyi sun afka wa kasashe daban daban na Turai. Ko da yake wadannan bala'i bala'i ne daga indallahi, amma lalata muhalli da 'yan Adam suka yi shi ma daya ne daga cikin dalilan da suka haifar da wadannan bala'i, musamman ma iska mai dumama yanayi da ake kara fitarwa ta kara dumama yanayi a duk duniya baki daya. Masanin ilmin yanayi Mohammad Reza Salamat ya yi gargadin cewa, 'mun lura da cewa, an yi ta samun dumamar yanayi a duk duniya, kuma saurinsa da yawansa duk sun jawo damuwar mutane.'

Masanan kimiyya sun nuna cewa, sabo da 'yan Adam sun dade suna amfani da albarkatun kasa fiye da kima, shi ya sa karfin garkuwa na muhalli ya ragu, har ma ya sa an yi ta samun bala'i masu tsanani kuma masu yawa. Sakamakon haka kuma, kewayen dan Adam ya lalace. Shugaban ofishin sakataren kula da rage bala'i na MDD, Salvano Bricano ya bayyana cewa, a cikin shekaru 10 da suka wuce, saurin lallacewar kewayen dan Adam ya fi na ko wane lokaci na da.

1  2