
A ran 6 ga wannan wata, gwamnatin kasar Eratrea ta aika sako zuwa ga kungiyar musamman ta Majalisar Dinkin Duniya don nemi ma'aikatan rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin duniya da ke tsugunewa a kasar Eratrea kuma suka zo ne daga kasar Amurka da Canada da Rasha da sauran kasashen Turai su janye jikinsu daga kasar a cikin kwanaki goma, a cikin sakon, ba ta fayyace kowane dalilin da ya sa ta yi haka ba, , wannan ya sa hali mai zafi da ake ciki a wasu watanni a iyakar da ke tsakanin kasar Eratrea da kasar Habasha ya kara tsanani. A ran 7 ga wannan wata, babban sakataren Majalisar dinkin duniya Kofi Annan ya bayar da sanarwa don la'anci gwamnatin kasar Eratrea cewa, kudurin da ta tsai da ya zama barna da ta yi ga cikakken ikon da kwamitin sulhu ya dora wa babban sakataren Majalisar Dinkin duniya wajen ba da jagoranci ga aikin kiyaye zaman lafiya . Ya nemi gwamnatin Eratrea da ta yi watsi da kudurin nan. A sa'I daya kuma, game da hali mai zafi da ake ciki na tsugunewar sojoji da yawa a iyakar da ke tsakanin kasar Habasha da Eratrea, Mr Annan ya aika Mr Guehenno da 'yan rakiyarsa zuwa kasashen biyu don shawo kansu.
A lokacin da Mr Guehenno ya yi ziyara a kasar Habasha da kasar Eratrea , ya gana da firayim ministan kasar Habasha, bangaren Habasha ya bayyana cewa, zai iya janye sojojinsa daga iyakar kasa bisa sharadin da ta gabatar, game da wannan Mr Guehenno ya nuna marabarsa, sa'anan kuma a lokacin da ya yi ziyara a kasar Eratrea, jami'an bangaren kasar Eratrea sun ki yin ganawa da Mr Guehenno. Bisa halin nan ne, Kwamitin sulhu ya tsai da kudurin janyewar wasu ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ke tsugunewa a iyakar da ke tsakanin kasashen biyu zuwa gefen kasar Habasha cikin gajeren lokaci a ran 14 ga wannan wata.
Dalilin da ya sa gwamnatin Eratrea ta kawo masifa ga ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya? Shi ne saboda gardamar da ake yi kan batun zana layin iyakar da ke tsakanin kasashen biyu.
'Yan kallo suna ganin cewa, kasashen biyu ba za su iya daidaita batun nan ba sai su daddale yarjejeniya kan iyakar da dukansu su amince da ita ta hanyar yin shawarwari bisa zaman daidai wa daida da sulhuntawar da gamayyar kasa da kasa suke yi.(Halima) 1 2
|