 A ran 15 ga wannan wata, wasu ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na kungiyar musamman ta Majalisar Dinkin Duniya da ke kasar Habasha da kasar Eratrea sun soma janye jikinsu daga kasar Eratrea, wannan ya alamanta cewa, kokarin neman sulhuntawa da mataimakin babban sakataren kula da harkokin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin duniya Jean Marie Guehenno ya yi bai sami sakamakon da ake son samuwa ba, halin da ake ciki a iyakar da ke tsakanin kasashen biyu ya kara tsanantawa.
A wannan rana, sojojin kiyaye zaman lafiya da yawansu ya kai 90 na Majalisar Dinkin Duniya na rukunin farko da suka zo daga kasar Amurka da Canada da kasashen Turai sun janye jikinsu daga birnin Asmera , hedkwatar kasar Eratrea zuwa birnin Adis Abeba, hedkwatar kasar Habasha. Mun sami labari cewa, bisa bukatar bangaren Eratrea ne, yawan ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da za su janye jikinsu daga kasar ya kai 180. A ran 14 ga wannan wata, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bayar da sanarwar shugaba, inda ta bayyana cewa, kudurin da kwamitin sulhu ya tsai da na janyewar ma'aikatan kiyaye zaman lafiya da ke kasar Eratrea musamman ne don ba da tabbaci ga kiyaye lafiyar ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya kawai. Halin da hukumar Eratrea take ciki na yin rashin hadin guiwa ya riga ya sa rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ba su iya aiwatar da dawainiyarsu sosai ba.
A ran 15 ga wannan wata a birnin Asmera, mataimakin sakataren Majalisar Dinkin Duniya da ke yin rangadin aiki a kasar Eratrea kan hali mai zafi da ake ciki a iyakar da ke tsakanin kasar Habasha da kasar Eratrea Jean Marie Guehenno ya bayyana a birnin Asmera cewa, dayake kiyewar da hukumar kasar Eratrea ta yi, shi ya sa ba ya sami damar ganawa da jami'an kasar Eratrea don shawo kan kasar da ta kawar da bukatarta ta janyewar ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ba.
1 2
|