Bayan 'hare-haren 11 ga Satumba' da aka kai wa kasar Amurka, jama'ar kasashen duniya suna nuna tausayi sosai ga kasar da jama'arta, kuma suna nuna goyon bayansu sosai ga matakan da ta dauka wajen yaki da ta'addanci, amma a cikin aikinta na yaki da ta'addanci, gwamnatin Bush ta dauki ma'aunoni biyu kuma ta kan dauki matakai da bangare daya, wannan ya bata manyan tsare-tsarenta na yaki da ta'addanci a duk duniya sosai, haka kuma wannan ya sa jama'ar kasar Amurka suna adawa da yaki sosai. A cikin wani kamfe na adawa da yaki, wata malama ta ce, 'Muna nan muna adawa da yaki, kai wa kasar Iraki yaki bai ci mutumci ba. Muna ganin cewa, abin muhimmanci a halin yanzu shi ne mu yi kokari domin hana mugun abu da ke faruwa a kasar Iraki.'
Kasashen duniya suna da ra'ayi daya cewa, ta'addanci ya riga ya zama abokan gaba na duk duniya, amma suna da bambancin ra'ayi wajen yadda aka kai farmaki ga ta'addanci da dai sauransu. Ko da yake haka ne, babban sakataren MDD Malam Kofi Annan yana ganin cewa, ya kamata kasashen duniya su gama kansu wajen yaki da ta'addanci, da haka ne kawai, za su iya kawar da ta'addanci da tabbatar da zama lafiyar jama'a a duk duniya. Ya ce, 'Muna ganin cewa, hadin kai a tasakanin kasa da kasa ya zama mafita ta kawai wajen cin nasarar yaki da ta'addanci. Na yi kira ga mambobin MDD da su daddale wata yarjejeniyar hadin kai a cikin hadin gwiwar kasashen duniya wajen yaki da ta'addanci.'(Danladi) 1 2
|