Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-14 17:39:05    
Aikin yaki da ta'addanci ya sami ci gaba daga mawuyacin hali

cri

Wannan shekarar da take kusan karewa da muke ciki, shekara ce ta hudu bayan da aka kai wa kasar Amurka 'hare-haren 11 ga Satumba'. A cikin shekaru hudu da suka gabata, aikin yaki da ta'addanci ya canja duniya, amma ba a sami zaman lafiya da jama'a suka fata ba. A shekarar 2005, an fi samun hare-haren da 'yan ta'adda suka yi a wurare daban daban a duk duniya.

A watan Yuli na bana, an kai farmakin ta'addanci a birnin London na kasar Ingila da kasar Massar; a watan Oktoba na bana, 'yan ta'adda sun kai hare-hare a tsibirin Bali da birnin New Delhi, babban birnin kasar India; a watan Nuwamba na bana, an kai farmakin kunar bakin wake a birnin Amman, babban birnin kasar Jordan. A sa'i daya kuma, a kasar Iraki, an kai farmakin ta'addanci ba lissaftuwa. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, a shekarar 2004, an kai farmakin ta'addanci da yawansu ya zarce 300, amma daga watan Janairu zuwa watan Oktoba na shekarar 2005, yawansu ya zarce 500, ta'addanci yana yaduwa sosai a duk duniya. Malam Li Wei, darektan cibiyar nazarin aikin yaki da ta'addanci ta hukumar nazarin dangantakar da ke tsakanin kasa da kasa ya bayyana cewa, farmakin ta'addanci da aka yi a bana suna da halin musamman idan aka kwatanta su da aka yi a da. Ya ce, 'Da farko dai, kungiyoyin ta'addanci suna taimakon juna. Ko da yake kungiyoyi daban daban sun kai farmakin ta'addanci ba bisa umurni irin daya ba, amma su kan taimaki juna domin ba da tasiri a duk duniya. Abu musamman na biyu shi ne, 'yan ta'adda masu yawa su ne matasa, wato shekarunsu sun ragu daga 30 zuwa 20 da haihuwa. Wannan ya bayyana cewa, matasa da yawa sun shiga cikin kungiyoyin ta'addanci ne bayan 'hare-haren 11 ga Satumba', haka kuma, kungiyoyin ta'addanci suna gaggauta bunkasa bayan 'hare-haren 11 ga Satumba'. Na uku shi ne, kungiyoyin ta'addanci sun fara horar da 'yan ta'adda a wurare daban daban, wadannan 'yan ta'adda su kan kai farmaki a yankinsu a maimakon sauran wurare.'

Shekarar 2005 shekara ce da gwamnatin Bush ta kara karfinta wajen yaki da ta'addanci, bisa rurin 'ciyar da dimokuradiyya gaba da kawar da ta'addanci sarai' da ta yi, sabo da haka, gwamnatin Bush ta sa kaimi sosai ga yunkurin dimokuradiyya a shiyyar Gabas ta tsakiya da ta tsohuwar tarayyar Soviet. Malam Xu Qinduo, wakilin gidan rediyon kasar Sin da ke kasar Amurka yana ganin cewa, a shekarar 2005, kasar Amurka ta sami nasara da hasara: ko da yake ta sami nasarori da yawa wajen shimfida dimokuiradiyya irin na Amurka a karkashin sunan yaki da ta'addanci, amma ta yi hasara sosai a fannonin hakkin 'dan Adam da kare mutumcin kasar Amurka da dai sauransu.

1  2