Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-08 17:31:12    
Girmama wa al'adu iri iri domin kafa wata duniyar da ke cike da jituwa tare

cri

A sa'i daya, Mr. Wen Jiabao ya jadadda cewa, kasar Sin wadda take yunkurin kawar da ita daga halin fama da talauci da neman bunkasuwa tana kawo wa sauran kasashen duniya babbar dama domin tana neman bunkasuwa cikin lumana. Mr. Wen ya kara da cewa,

"Kasar Sin tana tsaya tsayin daka kan bin hanyar neman bunkasuwa cikin lumana, kuma tana aiwatar da manufar bude kofa ga sauran kasashen duniya irin ta neman moriya da cin nasara tare. 'Yan kasa nagari na duk duniya sun gane cewa, bunkasuwar da kasar Sin ke samu wata babbar dama ce ga duk duniya, amma ba barazana ba. Halin zaman karko da kasar Sin ke ciki da bunkasuwar da ta samu babbar gudummawa ce da kasar Sin ta bayar ga zaman lafiya da bunkasuwar duk duniya. Ko da kasar Sin take daya daga cikin al'ummomin duniya, a cikin shekaru darurruka da suka wuce, ko da yake ta sha wahala kwarai, amma kasar Sin ta kan ciyar da al'adun duniya gaba a kullum. Bugu da kari kuma, al'ummar kasar Sin al'umma ce da ta fi son shimfida jituwa da zaman lafiya. Musamman cikin shekaru fiye da dari 1 da suka wuce, al'ummar kasar Sin ta sha wahaloli da yawa da masu hannu da shuni na sauran kasashen duniya suka kai mata, ta fi sanin cewa zaman lafiya tana da daraja kwarai. Kasar Sin ta bi hanyar neman bunkasuwa cikin lumana ne domin al'adu da tarihinta da halin da take ciki yanzu. Wannan wajababben zabe ne da kasar Sin ta yi. Sabo da haka, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka ta bi wannan hanya cikin dogon lokaci mai zuwa."  (Sanusi Chen)


1  2