Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-08 17:31:12    
Girmama wa al'adu iri iri domin kafa wata duniyar da ke cike da jituwa tare

cri

A ran 6 ga wata, firayin ministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao wanda ke yin ziyara a kasar Faransa ya bayar da wani jawabin da ke da lakabi haka: "Girmama wa al'adu iri iri domin kafa wata duniya mai jituwa tare" a jami'ar koyon ilmin kimiyya da fasaha ta Paris. A gaban dalibai fiye da dubu 1, bisa halin da ake ciki yanzu da tarihi, Mr. Wen Jiabao ya bayyana dalilai da abubuwan da suka wajaba ya kasance da al'adu da wayin kai iri iri. Ban da wannan, Mr. Wen ya bayyana harkokin cikin gida da na waje da kasar Sin take aiwatarwa ga dalibai. Sannan kuma ya yi hangen nesa ga makomar yin musayar al'adun kasar Sin da na kasar Faransa a nan gaba.

Da farko dai, Mr. Wen ya bayyana gudummawar da wayin kai iri iri suka bayar ga zaman al'ummar dan Adam. Mr. Wen ya ce, "Yanzu, wayin kai na dan Adam yana samun sauye-sauye kwarai. Ci gaban kimiyya da fasaha da musanye-musanyen tattalin arziki da al'adu suna rage bambancin da ke kasancewa a tsakanin wayin kai iri iri. Al'adun ko al'ummar kasar Sin ko al'ummar Faransa muke gada da koya dukkansu tushensu ne. Ya kasance da al'adu iri iri muhimmin hali ne na dan Adam."

Lokacin da yake tabo al'adun kasar Sin, Mr; Wen ya bayyana cewa, tushe da karfin ci gaban al'adun kasar Sin su ne muna da al'adar neman bunkasuwa da karfi cikin 'yancin kai kuma da al'adar bude tunani da amince da sauran al'adu daban-dabam kuma da ruhun neman yin sauye-sauye. A cikin jawabinsa, muhimmin abun da Mr. Wen ya bayyana shi ne manufar bude kofa ga kasashen waje da yin gyare-gyare kan tattalin arziki da kasar Sin ta fara dauka tun daga karshen shekaru 70 na karnin da ya gabata. Mr. Wen ya ce,

"Kasar Sin na yin gyare-gyare ne daga duk fanonni. Lokacin da muke yin gyare-gyare kan tsarin tattalin arziki, muna kokari kan yin gyare-gyare kan tsarin siyasa da tsarin raya al'adu da tsarin sarrafa zaman al'umma da dai sauransu. Makasudin aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen waje da yin gyare-gyare shi ne sa kaimi ga jama'a da su yi kokarin yin aikinsu domin kara raya karfin aikin kawo albarka, kuma biyan bukatu iri iri da jama'a suke nema a kai a kai."

1  2