Bisa labarin da aka bayar , an ce , An tsai da lokacin zaben shugaban kasar Azerbaijan a ran 19 ga watan Disamba na wannan shekara . 'Yan takara guda 6 ciki har da tsohon ministan kudi da ministan tsaron kasar za su yi gasar zaman shugaban kasar . Ko da ya ke daya ko biyu daga cikinsu suna nuna isa ga dimokuradiyyar kasashen yamma , amma duk da haka galibinsu suna kaunar kwanciyar hankali na tsarin Gamayyar kasashe masu mulkin kai .
Sabuwar jam'iyyar Azerbaijan ita ce jam'iyyar masu rashin shiga kowane rukuni bisa ka'idodjin siyasa da tattalin arziki da na zaman al'umma . Musamman a kan matsalar yaki da ta'addanci a Chechen na kasar Rasha suna rike da tsattsauran ra'ayoyi , kuma sun sha bamban da na jam'iyyu masu sassautan ra'ayoyi . Masanan binciken al'amuran duniya sun bayyana cewa , bisa fasahohin Shugaban kasar na yanzu a wajen tafiyar da harkokin gwamnatin kasar , a cikin 'yan shekarun da suka wuce , yana da tunanin tsare-tsaren musamman kan makomar kasarsa da yadda zai daidaita matsalar dake tsakanin kasarsa da kasashen yamma .
Game da tsarin dimokuradiyya, Shugaban kasar na yanzu yana da karfin siyasa da shugabanci wadanda 'yan takaransa suke karanci . Kafar watsa labaru ta kasar ta ce , Shugaban kasar wani shugaba ne wanda yake san yadda zai tsai da kuduri kuma yadda za a tafiyar da shi . Mutanen kasar suna ganin cewa , ba kawai yana da tunanin siyasa sosai ba , har ma yana da tsarin siyasa mai kyau . (Ado) 1 2
|