Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , a ran 5 ga watan nan , Kwamitin zaben tsakiyar kasar Khazakstan ya sanar da cewa , a cikin zaben da aka yi a ran 4 ga watan Nursultan Nazarbayev , shugaban kasar na yanzu ya sake zaman shugaban kasar da kuri'u na goyon baya na kashi 90 cikin 100 . Shi kansa ya bayyana wa manema labaru cewa , yau jama'ar Khazakstan za su tsai da zabe cewa , nan gaba wace irin kasa za su kafa ? Wace irin hanya za su tafiya ? Wane zaman yau da kullum mu da jikokinmu za su yi ? Na amince cewa , jama'ar kasar Khazakstan za su zabi kwanciyar hankali da yalwatuwar kasar .
Nasarar da Mr. Nazarbayev ya ci ta kawo karshen juyin juya hali mai launi da kasashen Yamma suke jira . Tun daga watan Nuwanba na shekarar 2003 zuwa watan Maris na wannan shekara , kasar Geogia da kasar Ukrain da kasar Kyrgyz bi da bi ne sun yi junyi juya hali mai launi . Saboda haka kasashen Yamma suna jiran sauran kasashen tsohuwar Tarayyar Soviet su ma za su yi irin wannan juyin juya hali .
1 2
|