Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-12-06 17:41:42    
Kasar Faransa da kasashen Afirka sun kara yin hadin guiwa domin fama da kalubalen da ke kasancewa a gabansu tare

cri

Sannan kuma, Mr. Chirac ya bayyana cewa, babban dalilin da ya sa samarin Afirka suka bar garinsu suka je kasar Faransa shi ne kasashensu suna cikin halin fama da talauci. Sabo da haka, muhimmiyar hanyar daidaita maganar makaurata ita ce bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka kuma da kubutar da su daga talauci. Tun da haka, Mr. Chirac ya shelanta cewa, yawan taimakon kudin da gwamnatin kasar Faransa za ta samar wa kasashe masu tasowa zai kai kashi 0.5 cikin kashi dari daga cikin jimlar kudaden samar da kayayyaki na kasa a shekara ta 2007. Ya zuwa shekara ta 2012, wannan adadi zai kai kashi 0.7 cikin kashi dari. Bugu da kari kuma, gwamnatin kasar Faransa ta tsai da kudurin cewa, za ta kara harajin tikitin jirgin sama tun daga watan Yuli na shekara ta 2006. An yi hasashen cewa, wannan yawan harajin tikitin jirgin sama zai iya kai kudin Euro wajen miliyan dari 2. Gwamnatin kasar Faransa za ta samar wa kasashen Afirka da suke fama da talauci wadannan kudade. Haka nan kuma, Mr. Chirac ya yi kira ga sauran kasashe masu ci gaba da su samar wa kasashen Afirka taimako kamar yadda kasar Faransa ke yi. A gun taron, yawancin kasashen Afirka sun yaba wa ra'ayoyin Mr. Chirac kwarai. Shugaba Amadou Toumani Toure na kasar Mali ya kuma ba da shawarar shirya taron makaurata a tsakanin Afirka da Turai domin kara tattaunawa kan maganar makaurata.

Ko da yake shugaba Laurent Gbagbo na kasar Kwadivuwa bai halarci taron ba, amma rikicin da ke kasancewa a kasar ya jawo hankulan shugabanni sosai, kuma ya zama daya daga cikin muhimman batuttukan da aka tattauna a gun taron. Dukkan shugabanni da firayin ministoci na kasashe dabam-daban sun tsai da kudurin cewa, za a hanzarta daidaita rikicin kasar Kwadivuwa domin tabbatar da zaman karko a yankin.

Bugu da kari kuma, a bayyane ne Mr. Chirac ya bayyana cewa, kasar Faransa ta nuna goyon baya ga Tarayyar Afirka da ta kafa wata rundunar tabbatar da zaman lafiya kafin shekara ta 2010. Mr. Chirac ya ce, yanzu kasar Faransa tana da sansanonin soja guda 5 a Afirka inda ke da sojojin Faransa fiye da dubu 10. Amma, sai rundunar soja ta tabbatar da zaman lafiya da Tarayyar Afirka za ta kafa ne za ta iya daukar nauyin tabbatar da zaman lafiya da na karko a nahiyar Afirka.

Bugu da kari kuma, Mr. Chirac yana fatan za a kara mai da hankali kan moriyar kasashen Afirka a gun taron ministoci na kungiyar WTO da za a yi a Hong Kong. Ya nuna cewa, manufar samar da kudin rangwame ga aikin gona da gwamnatin kasar Amurka ke dauka ta haddasa moriyar manoman kasashen Afirka.

Lokacin da yake jawabi, Mr. Toure na kasar Mali ya ce, ana noma auduga a kasashen Afirka 33. Amma domin kasashe masu ci gaba suna samar wa aikin gona kudin rangwame, manoman Afirka da suke noman auduga sun shiga cikin halin fama da talauci. Sauran shugabannin kasashen Afirka wadanda suka halarci taron sun kuma yi fatan za a sauya irin wannan halin da ake ciki a gun taron Hong Kong na kungiyar WTO.

To, jama'a masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen shirinmu na yau na Duniya ina Labari. Sanusi ya shirya muku wannan shiri kuma ke cewa mun gode muku kwarai da gaske domin sauraran da kuka yi. (Sanusi Chen)


1  2