 A ran 4 ga wata an rufe taron shugabannin kasar Faransa da kasashen Afirka na 23 wanda aka shafe kwanaki 2 ana yinsa a birnin Bamako na kasar Mali. Shugaba Jacques Chirac na kasar Faransa da shugabannin kasashen Afirka 53 sun halarci taron, kuma sun sami ra'ayi daya a kan maganganu da yawa. Manazarta sun bayyana cewa, wannan dai wani muhimmin taro ne da kasar Faransa da kasashen Afirka suka kara yin hadin guiwa iri ta gargajiya domin fama da kalubalen da ke kasancewa a gabansu tare.
A gun taron, shugabannin sun yi musayar ra'ayoyinsu kan halin dangantakar da ke tsakanin kasar Faransa da kasashen Afirka ke ciki da maganar yadda gwamnatocin kasashe masu ci gaba za su kara samar wa kasashen Afirka taimako da rage basusukan da suka ci kuma da maganar yadda za a cimma burin da aka tsara lokacin da ake shigo sabbin shekaru dubu-dubu.
Maganar makaurata muhimmiyar magana ce da ke kasancewa a gaban kasashen Afirka da kasar Faransa. Mr. Chirac ya nuna cewa, 'yan kwadago samari na Afirka sun bar garinsu, wannan ya sa tattalin arzikin kasashen Afirka bai iya samun ci gaba cikin sauri ba. A sa'i daya, bayan isowar samarin Afirka a kasar Faransa, suna fuskantar da matsalar samun aikin yi, suna kuma haddasa matsalolin zaman al'umma a kasar Faransa.
1 2
|