
A jihar Mongolia ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta a arewacin kasar Sin har yanzu akwai cututtukan annobar murar tsuntsaye. Bayan da aka bayar da Dokar gaggawa game da cututtukan dabbobi masu tsanani, Mr. Wang Junping, mataimakin darektan ofishin ba da umurni ga aikin rigakafin cututtukan tsuntsaye ya zanta da wakilin gidan rediyon kasar Sin cewa, wannan doka tana da muhimmancin gaske a wajen maganin cututtukan tsuntsaye. Ya ce, Wannan doka ta tanada alhakin da ke bisa wuyan gwamnatoci na matakai daban daban a fili. A cikin ayyukanmu na nan gaba, ya kamata mu yi kokarin cika alhakin da ke bisa wuyanmu don maganin cututtukan dabbobi masu tsanani. (Dogonyaro) 1 2
|