Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-08 16:43:53    
Sabon shawarwarin bangarori 6 ya jawo hankulan mutane sosai

cri

Matsalar nukiliya ta zirin tekun Korea ta arewa ta dangana ne da dangantakar da ke tsakanin kasar Korea ta arewa da korea ta kudu, da kuma zaman lafiya na dukan zirin tekun Korea. Sabo da haka, kasar Korea ta kudu ta yi ta aikin daidaitawa kan wannan matsala. Mr. Jin Dongguang, wakilinmu da ke zaune a kasar Korea ta kudu ya ce,

"Bayan da aka kammala shawarwarin bangarori 6 na karo na 4, a lokacin da ya ke yin magana da shugabannin kasashen da abin ya shafa ta waya, shugaban kasar Korea ta kudu ya bayyana cewa, kasar Korea ta kudu za ta ba da taimako yadda ya kamata tare da sauran kasashe don warware matsalar nukiliya ta zirin tekun Korea da wuri. Shugaban kungiyar wakilai na kasar Korea ta kudu ya kuma kai ziyara ga kasar Sin, da Amurka, da kuma sauran kasashe, ya bayyana manufar da bangaren Korea ta kudu ta tsaya kai, a sa'i daya kuma ya yi kokarin neman shirin aiwatar na haddadiyar sanarwa da bangarori dabam daban suka iya karba.

Kafin a kira shawarwarin bangarori 6 na karo na 5, kasar Japan da Korea ta arewa sun kuma yi cudanya na bangarori 2 tsakaninsu. Malama Wangying, wakiliyarmu da ke zaune a kasar Japan ta ce,

"A makon da ya wuce, kasar Korea ta arewa da Japan sun yi shawarwari na bangarori 2 a birnin Beijing. Kafin a soma sabon shawarwarin bangarori 6, cudanyar da kasar Korea ra arewa da Japan suka yi ta kafa muhalli mai kyau ga shawarwarin, sun yi kokarin warware matsalar da ke tsakaninsu kafin shawarwarin bangarori dabam daban, wannan ya hana iyuwar shiga halin kaka-ni-ka-yi."

Kasar Rasha kuma ta nuna maraba sosai ga shawarwarin bangarori 6 na karo na 5.

Amma, kasar Korea ta arewa da Amurka suna nuna rashin amincewar juna kan wasu muhimman matsaloli, kuma suna tsayawa kan ra'ayoyinsu. Ko da ya ke sun yi cudanya sau da yawa a cikin watan da ya wuce, amma ba su rage bambanci da ke kasancewa a tsakaninsu ba.

Watakila wannan zai kawo tasiri ga shawarwarin bangarori 6 na karo na 5, kai tsaye. Mai yiyuwa ne sabon shawarwarin zai zama mafi wuya fiye da na da. Ra'ayoyin jama'a na nuna fatan bangarori dabam daban za su kara fahimfar juna da nuna amincewar juna a cikin wannan shawarwarin. (Bilkisu)


1  2