Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-11-08 16:43:53    
Sabon shawarwarin bangarori 6 ya jawo hankulan mutane sosai

cri

Ran 9 ga wata, za a yi sabon shawarwarin bangarori 6 dangane da matsalar nukiliya ta zirin tekun Korea a nan birnin Beijing. Bisa tushen haddadiyar sanarwar da shawarwarin bangarori 6 na karo na 4 suka bayar wanda aka rufe shi a ran 19 ga watan Satumba, shawarwarin nan zai ci gaba da yin tattaunawa kan shirin aiwatarwa da sanarwar, da kuma hakikanan matsalolin da ke jawo hankulan bangarori dabam daban. Bangarori dabam daban suna sa ido kan wannan shawarwari da fatan zai sami hakikanin ci gaba wajen warware muhimman matsaloli. Domin samar da shawarwarin da zai sami ci gaba, wane kokari ne bangarori dabam daban suka yi? Kuma ko sabon shawarwarin bangarori 6 zai iya samun ci gaba? Wakilinmu ya kai ziyara ga maneman labaru na redionmu da ke zaune a kasar Korea ta kudu, da Japan, da Amurka da Rasha, da kuma wata da ta taba halartar shawarwarin sau da yawa, wato malama Pan Xiaoying.

Domin shirya shawarwarin bangarori 6 na karo na 5, kasar Sin ta yi cudanya sosai da sauran bangarori 5. Malama Pan Xiaoying ta ce,

"Bayan da aka kammala shawarwarin bangarori 5 na karo na 4, Mr. Libin, jakadar ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin mai kula da sha'anin zirin tekun Korea ya kai ziyara ga kasar Korea ta arewa, da Amurka, da Korea ta kudu daya bayan daya. A karshen watan Oktoba, Mr. Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na J.K.S. ya taba kai ziyara ga Korea ta arewa, inda ya yi musayen ra'ayoyi da Mr. Kim Jong il, gaba daya bangarorin nan biyu suna ganin cewa, shawarwarin bangarorin 6 na karo na 4 ya sami sakamako sosai, za su tabbatar da haddadiyar sanarwar da aka daddale a gun shawarwarin, da kuma ci gaba da yin kokari don tabbatar da burin rashin nukiliya a zirin tekun Korea. A cikin 'yan kwanakin da suka wuce, Mr. Wu Dawei, mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin ya gana da Kenichiro sasae, shugaban kungiyar wakilai na kasar Japan da ke hallartar shawarwarin bangarori 6, inda suka yi musayen ra'ayoyinsu kan shawarwarin na karo na 5. Bayan haka kuma, bangaren Sin da Rasha su ma sun yi cudanya tsakaninsu. Sabo da haka, ana iya cewa, bangaren Sin ya kafa muhalli mai kyau kan shirya shawarwarin bangarori 6 na karo na 5."

1  2