Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-10-28 15:30:45    
Sojojin sama na kasar Isra'ila sun kai farmaki ga zirin Gaza

cri

Bayan da aka yi fashewar bom ta kunar bakin wake a birnin Hadera da ke bakin teku na kasar Isra'ila, sai nan da nan gwamnatin kasar ta yanke shawarar daukan matakan soja kan Palesdinu. Ban da farmakin da sojojinta suka kai wa zirin Gaza, a ran 27 ga wata, sojojinta sun kama wani babban shugaban kungiyar Jihad. Bangaren sojojin kasar Isra'ila ya bayyana cewa, makasudin wannan aiki shi ne kai naushi ga kungiyar Jihad, haka kuma za a gudanar da shi a yankuna biyu. Na daya shi ne arewacin zirin Gaza, za a kai naushi ga dakarun Palesdinu da ke Qassam domin shara fage ga sojojinta da su kai hari a zirin Gaza. Na biyu shi ne birnin Jenin da na Tul Karm da ke yammacin gabar kogin Jordan da kauyukan da ke kewayensu, za a kama mambobin kungiyar Jihad.

A ran 27 ga wata, firayin minstan kasar Isra'ila Sharon ya bayyana cewa, kasar za ta ci gaba da daukan matakin soja har sai dakarun Palesdinu sun daina yin ayyukan ta'addanci. Ya ce, a halin yanzu da ake ciki, ba zai gana da shugaban hukumar ikon al'umma ta Palasdinu Mr Abbas ba. Sai da in Abbas ya kai babban naushi ga kungiyoyin dakaru, in ba haka ba, ba za a sami ci gaba a yunkurin shimfida zaman lafiya a tsakanin Palesdinu da Isra'ila ba. Bisa shirin da aka yi, Sharon da Abbas za su yi shawarwari a tsakiyar wannan wata domin tattauna yadda aka sa kaimi ga yunkurin shimfida zaman lafiya bayan da aka gudanar da shirin janye jiki na bangare daya. A farkon wannan wata da muke ciki, sabo da kasancewar bambancin ra'ayi a kan wasu manayan abubuwa, shi ya sa suka jinkirtar da lokacin ganawar zuwa karshen watan nan ko farkon watan Nuwamba.

A ran 27 ga wata, firayin ministan Palesdinu Ahmed Qurai ya bayyana cewa, martani mai tsanani da kasar Isra'ila ta mayar ga fashewar bom ta kunar bakin wake da aka kai wa birnin Hadera zai kazanta halin da ake ciki ne a bangarorin biyu kawai. A ran nan a yayin da shugaban kasar Massar Mubarak ke amsa tambayoyin da kafofin watsa labarai na kasar Isra'ila suka yi masa, ya ce, kasar Isra'ila tana bukatar Abbs, sabo da haka, ya kamata ta taimaka masa ya karfafa kwarjininsa a idanun jama'ar Palesdinu. Ya ci gaba da cewa, idan kasar Isra'ila ta dauki aikin kwance damarar kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi na Palesdinu a matsayin sharadin sa kaimi ga yunkurin shimfida zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu, to, watakila wannan zai haddasa yakin basasa a Palesdinu.(Danladi)


1  2