Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-10-28 15:30:45    
Sojojin sama na kasar Isra'ila sun kai farmaki ga zirin Gaza

cri

A ran 27 ga wata da dare, sojojin sama na kasar Isra'ila sun kai farmaki a kan barikin 'yan gudun hijira na Shadi Mohanna da ke arewacin zirin Gaza, wannan ya sa Palesdinawa da yawansu ya kai 7 sun mutu, biyu daga cikinsu su manyan shagabannin kungiyar Jihad ne. Isra'ila ta dauki wannan mataki ne domin mayar da martani ga fashewar bom ta kunar bakin wake da aka kai wa birnin Hadera da ke bakin teku na kasar Isra'ila.

A daidai wannan lokaci, ganawar da firayin ministan kasar Isra'ila Sharon da shugaban hukumar ikon al'umma ta Palasdinu Abbas suka yi shirin yi ba ta da makoma a sakamakon hali mai kara tabarbarewa da ake ciki. Haka kuma wannan ya kalubalanci yarjejeniyar fahimtar juna da tsagaita wuta da bangarorin biyu suka daddale a watan Fabrairu na bana.

Wani mutumin da ya ga al'amarin ya ce, wani jirgin sama na kasar Isra'ila wanda babu mutane a ciki ne ya harba wani harsashi mai linzami kan wata mota da ke tafiya a barikin, sabo da haka, wani shugaban kungiyar Jihad da mataimakinsa sun rasa rayukansu. Wannan kuma ya haddasa mutuwar farar hulu da yawansu ya kai biyar, cikinsu akwai wani yaro mai shekaru 15 da haihuwa. Bayan haka, bangaren sojojin kasar Isra'ila ya bayar da wata sanarwa inda ya amince da cewa, ya riga ya dauki mataki ga shugabannin kungiyar Jihad. Bangaren sojojin kasar Isra'ila ya zargi wannan shugaban kungiyar Jihad da ya saba wa yarjejeniyar tsagaita wuta, kuma ya shugabanci sojojinsa da su harba rokoki  zuwa kudancin kasar Isra'ila.

A ran nan, wani kakakin kungiyar Jihad ya sanar da cewa, kungiyar za ta mayar da martani mai tsanani kan Isra'ila. A sa'i daya kuma, wani shugaban kungiyar dakaru mai suna al-Aqsa Martyrs' Brigade na Palesdinu ya bayyana cewa, kungiyar ba za ta girmama yarjejeniyar tsagaita wuta da ta daddale da Isra'ila ba.


1  2