 A ran 23 ga wata, wani jami'in gwamnatin Nijeriya ya sanar da cewa, fasinjoji da ma'aikata wadanda yawansu ya kai 117 da ke cikin wani jirgin saman fasinja wanda ya fadi a ran 22 ga wata da dare dukkansu sun mutu. Wannan ya zama hadari mai tsanani na karo na 2 da ya faru cikin shekaru 3 da suka wuce a Nijeriya.
A ran 22 ga wata da dare, wani jirgin sama kirar Boeing 737- 200 wanda ke dauke da ma'aikata 6 da fasinjoji 111 ya tashi daga Lagos, hedkwatar tattalin arziki na Nijeriya zuwa Abuja, hedkwatar kasar, ba da dadewa ba bayan da jirgin saman ya tashi sai matukin ya bai wa tashar kasa lambar neman ceto, daga baya sai ya kasa yin cudanya da tashar sarrafawa da ke kasa, kuma ya fadi cikin wani gandun daji da ke arewa maso yammacin babban filin jirgin sama na Lagos da misalin kilomita 30. An sami wani rami wanda fadinsa ya kai mita 25 kuma zurfinsa ya kai mita 10 sabo da faduwar jirgin saman, jirgin saman ya kone cikin ramin. Motar yin ceto ba ta iya shiga cikin ramin don yin ceto ba. Ade aboluyrin, babban kwamandan hukumar tsaron kasa da zamaan lafiyar jama'a na Nijeriya ya gaya wa manema labaru a wurin cewa, "Sabo da duk jirgin saman ya nutse ciki ramin, shi ya sa duk mutanen da ke ciki sun mutu, ba mai yiwuwa ba ne a sami wanda yake da rai".
A wannan rana ofishin Olusegun Obasanjo, shugaban kasar Nijeriya ya ba da sanarwa cewa, shugaba Obasanjo shi kansa ne yake sa ido kan aikin yin ceto. Jami'an zirga-zirgar jiragen sama na kasar suna nan suna ta neman bakin akwati wanda a ciki ake samun bayanin zirga-zirgar jirgin saman. Bisa kwarya kwaryar binciken da aka yi an ce, dalilin da ya sa wannan hadarin jirgin saman fasinja ya auku shi ne sabo da mumunan yanayin sama a ran 22 ga wata da dare ko kuma sabo da lalacewar wannan jirgin sama.

An labarta cewa, a cikin wannan jirgin sama da akwai wasu manyan jami'an gwamnatin Nijeriya, amma har yanzu ba a san hakikanan mukanansu ba tukuna. Kuma an ce akwai wasu fasinjoji na kasashen waje, amma ba a san su wane ne ba.
An ce, a birnin Lagos da akwai Sinawa 'yan kasashen waje da 'ya'yan Sinawa mazauna kasashen waje fiye da dubu 30 da suke zaune a birnin Lagos, bayan aukuwar wannna hadari jami'an babban ofishin Consulate na kasar Sin da ke Lagos sun mai da muhimmanci sosai kan wannan hadari. Bayan da suka duba sunayen fasinjojin da filin jirgin sama ya bayar cikin tsanaki, sun tabbatar da cewa, babu Sinawa a cikin mutanen da ke cikin wannan jirgin sama.
Wannan ya zama hadari mai tsanani na karo na 2 da ya faru cikin shekaru 3 da suka wuce wanda kuma ya kai naushin tsiya ga sha'anin zirga-zirgar jiragen sama na kasar Nijeriya. A ran 4 ga watan Mayu na shekarar 2002, wani jirgin saman fasinja na cikin kasar Nijeriya ya fadi a wata unguwar da mutane masu yawa ke zaune ta birnin Kano da ke arewacin kasar, wanda kuma ya haddasa mutuwar a kalla mutane 180. Manazarta sun bayyana cewa, sabo da matsalolin da ake gamuwa da su wajen kayayyaki da sarrafa harkokin da kuma kudi, shi ya sa yanzu ya kasance da wasu matsalolin kwanciyar hankali wajen sha'anin zirga-zirgar jiragen sama na cikin kasar Nijeriya.
Daga tsakiyar shekaru na 80 na karni na 20 gwamnatin Nijeriya ta sassauta sarrafawar da ta yi wa sha'anin zirga-zirgar jiragen sama, wato ta fara tafiyar da tsarin makasusi ga wannan sha'ani zuwa yanzu, yawan kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama masu zaman kansu da aka kafa cikin kasar Nijeriya ya kai fiye da 10, amma sabo da karancin kudi, shi ya sa kamfanoni da yawa suka ga tilas ne su sayi ire iren jiragen sama da kamfanonin jiragen sama na Turai da na Amurka suka kawar da su. Wannan babban dalilin ke nan da ya jawo matsalolin kwanciyar hankali na zirga-ziragar jiragen sama na kasar Nijeriya. (Umaru)
Kasar Nijeriya za ta soma zaman makoki saboda mutanen da suka rasu a cikin hadarin faduwar jirgin sama
|