A ran 24 ga wata gwamnatin kasar Nijeriya ta shelanta cewa, tun daga wannan rana ne za a soma zaman makoki saboda mutanen da suka rasu a cikin hadarin faduwar jirgin sama da ta auku a ran 22 ga wata da dare har na tsawon kwanaki 3.
Lokacin da ake zaman makokin, za a saukar da tutar Nijeriya kasa kasa, kuma za a shirya wasu bukukuwa domin addu'a. Shugaba Olusegun Obasanjo na kasar Nijeriya ya yi kira ga jama'a da su yi addu'a don mutane wadanda suka rasu a cikin hadarin da iyalansu.
A ran 22 ga wata da dare, wani jirgin saman fasinja kirar Boeing 737 na kamfanin Bellview mai zaman kansa ya fadi a wurin da ke da nisan kilomita 30 daga filin jirgin sama na Murtala Mohammed na Lagos. Mutane 117 ciki har da ma'aikata 6 na jirgin saman dukkansu sun rasu.
Yanzu, hukumar Nijeriya da abin ya shafa tana binciken dalilin da ya sa aukuwar hadarin kuma tana yin aikin tantance asalin mutanen da suka rasu a cikin hadarin. (Sanusi Chen)
|