Na farko, an riga an kammala babbar dawainiya a majalisar dokoki ta wucin gadi, shi ya sa Koizumi Junichiro ya yi tsammanin cewa, yana iya sarrafa harkokin siyasa a kasar Japan, shi ya sa ya kai ziyarar a haikalin ba tare da tsoron kome ba don neman samun goyon baya daga wajen rukunin masu tsattsauran ra'ayi, wani dalilin daban kuma shi ne koizumi Junichiro zai yi wa majalisar ministoci garambawul a watan Nuwamba, wannan sabuwar alama ce da ya nuna ga sabuwar Majalisar ministoci, kuma wani kokari ne da ya yi wajen diplomasiya da tsaron kai da sha'anin soja don bayyana cewa, zai aiwatar da manufar diplomasiya yadda ya ga dama.
Mr Gao Hong ya bayyana cewa, Ban da wadannan dalilai, har ma da wassu dalilan hakika , daga cikinsu, da akwai wani dalilin da ya sa ya kai ziyarar a ran 17, shi ne saboda ranar nan rana ce da kumbon kirar Shenzhou mai lamba 6 kuma mai dauke da 'yan sama jannati na kasar Sin ya dawo kasar tare da nasara. Jama'ar kasar Sin sun mai da hankali ga ala'marin nan , game da wannan, ana iya cewa, a kan batun nan, Koizumi Junichiro ya kulla makirci tun tuni, amma ba zai sami kome ba.
Game da yadda huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Japan za ta kasance, wani furefesa mai suna Su Zhiliang ya bayyana cewa, kasar Sin da kasar Japan suna makwabtaka da juna, suna da moriya iri daya, ya kamata kasashen biyu su kara hadin guiwa a tsakaninsu a kowace rana, kuma su sami ra'ayi daya a kan manyan matsaloli. Ya kira gwamnatin kasar Japan da cewa, ya kamata ta mai da muhimmanci ga makomar nan gaba da kuma daidaita matsalolin da aka bari a tarihi yadda ya kamata.(Halima) 1 2
|