Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-10-19 17:55:58    
Ziyarar nuna ban girma da Koizumi Junichiro ya yi a haikalin Yasukuni aikin jahilci ne

cri
Firayim ministan kasar Japan Koizumi Junichiro ya biris da kiyewa mai zafi da ra'ayoyin jama'a na gida da na waje suka yi masa , ya kai ziyarar nuna ban girma a haikalin yasukuni don tunawa da masu laifufukan yakin duniya na biyu da ke bisa matsayin A a ran 17 ga wannan wata . Wannan karo na biyar ne da ya yi ziyarar nuna ban girma a haikalin Yasukuni tun daga watan Afril da ya hau mukamin kujerar firayim ministan kasar. Ina dalilin da ya sa ya yi taurin kai haka wajen kai ziyarar nuna ban girma a haikalin? Kuma me ya sa ya zabi ran 17 ga wannan wata don kai ziyarar a haikalin? Game da batuttuwan nan, wani masanin aikin bincike na cibiyar nazarin kimiyyar zamantakewar al'umma ta kasar Sin Mr Gao Hong ya bayyana cewa, kai ziyarar nuna ban girma a haikalin Yasukuni don tunawa da masu laifufuka na yakin duniya na biyu da ke bisa matsayin "A" , ba ma kawai ya bata zuciyar jama'ar kasashen da ke makwabtaka da kasar Japan ba, hatta ma yana zuga kasar Japan da ta kama wata hanyar kuskure. Aikin da Koizumi Junichiro ya yi aiki ne na kuskure, ya kamata a yi masa suka sosai  kuma zarge shi sosai da sosai.

Lokacin da Gao Hong ya tabo magana a kan dalilan da ya sa Koizumi Junichiro ya kai ziyarar a haikalin, ya bayyana cewa, wajen koizumi Junichiro, don aiwatar da tafarkinsa da ra'ayinsa wajen siyasa da kuma cim ma burin mayar da kasar Japan ta zama babbar kasa wajen harkokin siyasa da sha'anin soja, sai shi da kansa ya kira da kuma ba da misali don tayar da tsumin al'umma na wai  kishin kasa a cikin zuciyar jama'a farar hula, game da wannan , ko shakka babu aikin kuskure ne da ya yi .

Mr Gao Hong ya bayyana cewa, akwai wasu dalilan da ya sa Koizumi Junichiro ya zabi ran 17 ga wannan wata don kai ziyarar nuna ban girma a haikalin Yasukuni.


1  2