Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-10-18 17:36:26    
Tafiye tafiyen kumbo mai daukan mutane na karo na biyu da kasar Sin ta yi ya sami cikakkiyar nasara

cri

Jama'a masu karatu, yanzu ga shirinmu na duniya ina labari na yau: Bayan da aka yi zirga zirga cikin kwanaki biyar, a ran l7 ga watafn da Asuba agogon birnin Beijing, kumbo mai daukan 'yan sama jannati biyu mai lambar "Shenzhou" 6 wanda kasar Sin ita kanta ta tsara fasali da kera shi ya koma kan wurin da aka tsaida tare da nasara, Kana kuma halayen jikin 'yan sama jannati guda biyu suna da lafiya da kyau. Daga nan ne babban shugaba mai ba da jagora ga aikin tafiye tafiye na kumbo mai daukan mutane na karo na biyu na kasar Sin ya bayyana cewa, tafiye tafiyen kumbo mai daukan mutane na karo na biyu da kasar Sin ta yi ya sami cikakkiyar nasara. Bugu da kari kuma, a yau da safe, a gun taron ganawa da maneman labaru da ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa na kasar Sin ya shirya, wani jami'I na sashen zirga zirgar kumbo mai daukan mutane a cikin sararin samaniya na kasar Sin ya bayyana cewa, bisa shirin da aka yi an ce, a wajen shekara ta 2007, kasar Sin za ta nuna tabbaci ga yadda 'yan sama jannati na kasar Sin za su fito daga kumbo, har za su yi tafiye tafiye a sararin samaniya. Yanzu ga abubuwan da wakiliyar rediyon kasar Sin ta rubuto mana filla filla.

Jama'a masu karatu, ni ce wakiliyar rediyon kasar Sin daga cibiyar kula da aikin zirga zirga masu daukan mutane a cikin sararin samaniya na birnin Beijing ina bayyana muku wannan labari.Yau da Asuba da karfe 4 da minti 33,a muhimmin wurin saukawa da aka tsaida a jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta dake arewancin kasar Sin,kumbo mai daukan mutane mai lamba "Shenzhou" shida ya sauka tare da nasara. Ga 'yan sama jannati guda biyu sun fito daga kumbo,Yanzu a duk cibiyar kula da aikin zirga zirga mai daukan mutane a cikin sararin samaniya, ga mutane suna farin ciki sosai, cike da fara'a ne sun yi hannu bibbiyu cikin dogon lokaci don murnar babbar nasarar da aka samu wajen yin zirga zirga na kambo mai daukan mutane na karo na biyu a cikin sararin samaniya.


1  2  3