Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-10-03 20:59:11    
Wani Muhimmin matakin da kasar Algeria ke dauka domin kau da tarkacen 'yan ta'adda

cri

Bayan da Mr. Bouteflika ya zama shugaban kasar a cikin shekara ta 1999, ya dauki matakai da dama domin mayar da zaman lafiya da zaman karko a cikin kasar. Kuma a cikin waccan shekara, an zartas da "dokar samun sulhuntawa ta dukkan jama'ar kasa " ta hanyar kuri'ar raba gardama, wadda ta taka muhimmiyar rawa kan tsoratar da kungiyoyin ta'addanci da kuma murkushe su, ta haka halin tsaron kasar da ake ciki a wancan lokaci ya samu kyatatuwa, amma ba a kawar da farmakin nuna karfin tuwo kwata kwata ba.

Domin karfafa sakamakon da aka samu daga dokar samun sulhuntawa ta dukkan jama'ar kasar, gwamnatin da Mr. Bouteflika ke shugabanta tana fatan za a ci gaba da murkushe kungiyoyin ta'addanci ta hanyar jefa kuri'ar raba gardama kan "shirin shawarar samun sulhuntawar al'umma da dokokin zaman lafiya", ta yadda za a kau da al'amuran nuna karfin tuwo kwata kwata.

Kafin jefa kuri'ar raba gardama, manyan jami'ai ciki har da shugaba Bouteflika sun je wurare daban daban cikin kasar domin yin bayani kan shirin. A ran 26 ga wata, Mr. Bouteflika ya yi jawabi a gun wani taron da aka yi a birnin Algeris, babban birnin kasar Algeria, cewa al'amuran nuna karfin tuwo da 'yan ta'adda suka yi a cikin kasar a cikin shekaru fiye da goma da suka wuce sun taka mummunar rawa ga kasar, shi ya sa tilas ne a sa aya ga abubuwan bakin ciki na lokacin ta hanyar samun sulhuntawar al'umma domin tabbatar da samun zaman lafiya a kasar. A sa'i daya kuma ya jaddada cewa, kasar ta gabatar da shirin nan ba zai shaida cewa, gwamnatin kasar ba ta da karfi, rundunar dakarun kasar za ta kai wa dakaru masu taurin kai farmaki.

Amma wasu kungiyoyin 'yan hamayya na kasar sun ki yarda da jefa kuri'ar raba gardama. Kuma sun bayyana cewa, shirin zai sa 'yan rundunar tsaron kasar masu yawa wadanda suka taba yin al'amuran karya doka su magance hukuncin da za a kai musu.(Kande Gao)


1  2