A ran 29 ga watan nan da dare, an jefa kuri'ar raba gardama a kasar Algeria kan "shirin shawarar samun sulhuntawar al'umma da dokokin zaman lafiya". Wanna wani muhimmin mataki ne da kasar Algeria ke dauka domin kau da tarkacen 'yan ta'adda, kuma makasudin daukar matakin nan shi ne sa aya ga al'amuran nuna karfin tuwo da 'yan ta'adda ke yi wa kasar a cikin shekarun nan da yawa da kuma samun zaman lafiya da sultuntawar duk kasar.
Bisa abubuwan da aka tanada cikin shirin shawarar samun sulhuntawar al'umma da dokokin zaman lafiya, an ce, ba za a yanke hukunci ga wadanda suka mika makamai don daina daukar matakan dakaranci da wadanda suka ba da kai da ake neman kama su ba, amma ban da wadanda suka yi kisan kiyashi da fyade da kuma jefa boma-bomai a wuraren jama'a. bugu da kari kuma, gwamnatin kasar za ta ba da taimakon agaji ga iyalan musulmai masu tsattsauran ra'ayi.
A cikin karshen shekaru 80 na karnin da ya gabata, sabo da tsanancewar halin tattalin arziki da kasar ke ciki da kuma mugun tasiri daga kasashen waje kan samun demokuradiyya, kasar Algeria tana da matsalolin siyasa da zamantakewar al'umma masu tsanani sosai.
1 2
|