
Mr. Paul Martin, firayim ministan kasar Canada ya ce, Kafa muhimmiyar dangantakar abokantaka tana nufin cewa, za mu yi gama kai a fannoni mafiya yawa, wato daga siyasa har zuwa sabon makamashi da sabbin fasahohi da kiyaye muhalli, kuma za mu yi gama kai a harkokin kasashen duniya, misali gyare gyaren MDD da maganar sauyawar yanayi. A ganinmu Sin da Canada suna da fifiko.
Ban da haka kuma a gun wannan ziyara shugaba Hu Jintao ya sake nanata matsayi da ra'ayi na bangaren kasar Sin. Ya ce, Tsayawa kan manufar kasar Sin da amincewa da Taiwan ita ce wani kashin da ba a iya balle shi daga yankin kasar Sin ra'ayi daya ne na kasashen duniya, ciki har da kasar Canada. Dalilin da ya sa dangantakar da ke tsakanin Sin da Canada ta yi ta samun ci gaba shi ne sabo da gwamnatocin kasar Canada duk sun tsaya kan matsayin gaskiya. Kwanakin baya a cikin kasar Canada wasu mutane sun yi surutu kan maganar Taiwan, muna fatan gwamnatin Canada za ta daidaita wannan magana da kyau. Kada a tauye tushen siyasa na dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasar Canada. (Dogonyaro) 1 2
|