Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-09-13 17:13:19    
Shugaba Hu Jintao ya samu babbar nasara a gun ziyarar da ya yi a kasar Canada

cri

Daga ran 8 zuwa 11 ga watan nan shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya ziyarci Ottawa, babban birnin kasar Canada da Toronto, birnin da ya fi girma a kasar. A cikin wannan ziyarar da shugaba Hu Jintao ya yi ya yi shawarwari da shugabannin kasar Canada, ya halarci dandalin tattaunawar tattalin arziki da ciniki na Sin da Canada da aka yi a hedkwatar kasa kuma ya bayar da jawabi. Shugaba Hu Jintao ya riga ya samu manyan nasarori a gun ziyara da ya yi a Canada.

Wannan ziyarar da shugaba Hu Jintao ya yi a kasar Canada ita ce ta farko da shugaban kasar Sin ya yi a Canada a shekaru 8 da suka shige. Muhimmin sakamakon da aka samu a gun wannan ziyara shi ne an ciyar da dangantakar da ke tsakanin Sin da Canada daga dangantakar abokantaka ta gama kai a duk fannoni zuwa muhimmiyar dangantakar abokantaka.

A shekaru 35 da aka kulla huldar jakadanci dangantakar da ke tsakanin Sin da Canada ta samu babban ci gaba. An yi ta karfafa cudanya da gama kai a duk fannoni, jama'ar kasashen biyu sun samu moriya mai tsoka. A lokacin da aka kulla huldar jakadanci, darajar cinikin da aka yi a tsakanin bangarorin biyu ita ce dollar miliyan 150, amma a shekarar bara ta kai dollar biliyan 15.5. Shugaba Hu Jintao da gaske ne ya sanar da cewa, Gaba dayanmu mun yarda da ciyar da dangantakar da ke tsakanin Sin da Canada zuwa muhimmiyar dangantakar abokantaka don karfafa gama kai na bangarorin biyu da yalwata dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu har dogon lokaci.


1  2