
An shirya bikin jana'izarta a ran 20 ga watan Agusta da safe, mijinta He Qingkui da shahararrun 'yan wasan kwayikwayo Zhao Benshan da Song Dandan da Fan Wei da dai sauransu sun halarci bikin. Shugabannin da suka zo daga hukumar al'adu ta lardin Jilin da gwamnatocin daban daban na lardin su ma sun halarci bikin jana'iza. Abin lura shi ne, a gun bikin, dubban jama'a sun yi ta kuka har ba a iya shawo kansu ba.(Danladi) 1 2 3
|