
A ran 24 ga wata, jam'iyya mafi girma ta rukunin Sunni, wato jam'iyyar musulmi ta Iraki da taron jama'ar rukunin sunni wanda ke kunshe da kungiyoyin rukunin Sunni da dama da kungiyar malaman musulmi da dai sauran kungiyoyin siyasa na rukunin Sunni sun nuna adawa ga tsarin tarayya bi da bi, kuma sun ki amincewa da daftarin sabon tsarin mulki. Shugaban taron jama'ar rukunin Sunni na Iraki, Adnan al-Dulaimi ya bayyana cewa, daftarin tsarin mulki da aka gabatar ga majalisar wucin gadi a ran 22 ga wata ya fito ne bisa shawarwarin da aka yi tsakanin kawancen hadin kan rukunin Shi'a da tarayyar Kurdawa ne kawai, wanda bai dace da doka ba. Ya jaddada cewa, dukan jama'ar Iraki suna da ikon mallakar albarkatun kasa na Iraki, aiwatar da tsarin tarayya a arewacin Iraki ko kudancinta zai kawo baraka a kasar Iraki.
A waje daya kuma, majalisar yankin Kurdawa ta zartas da daftarin tsarin mulki a ran 24 ga wata, inda ta tsaya kan kiyaye tsarin tarayya. Shugaban majalisar, Adnan al-Mufti ya bayyana cewa, ko da yake daftarin bai cika burin Kurdawa sosai ba, amma shi babban ci gaba ne da aka samu a fagen siyasa.
1 2 3
|