
Sabo da har zuwa yanzu dai rukunoni daban daban na Iraki ba su cimma daidaito a kan daftarin tsarin mulki ba, a ran 25 ga wata, majalisar wucin gadi ta Iraki ta soke jefa kuri'a da da ma aka yi shirin yinsa a kan daftarin tsarin mulki a ran nan. A ran 26 ga wata da safe, shugaban majalisar wucin gadi Hajem al-Hussani ya shelanta cewa, za a dakatar da kada kuri'a a kan daftarin sabon tsarin mulki da kwana daya, ta yadda shugabannin rukunoni daban daban za su kau da bambancin ra'ayi tsakaninsu.
To, wannan shi ya zamo karo na uku da majalisar wucin gadi ta Iraki take dakatar da jefa kuri'a a kan daftarin tsarin mulki.
A halin yanzu dai, sabanin ra'ayin da ke tsakanin rukunoni daban daban dangane da tsarin mulki yana kasancewa musamman a kan maganar tsarin tarayya. Musulmi na rukunin Sunni suna adawa da tafiyar da tsarin tarayya, a ganinsu, wannan zai jawo baraka a kasar, har kullum dai suna tsayawa tsayin daka a kan aiwatar da tsarin rike iko a tsakiya, kuma suna son a danka ikon kulawa da kudaden shiga na man fetur da kuma rarraba su a hannun gwamnatin kasar. A sa'i daya kuma, musulmi na darikar Shi'a da kurdawa suna goyon bayan tsarin tarayya. Amma ko da yake rukunin Shi'a da Kurdawa suna da kujeru sama da 210 daga cikin kujeru 270 a majalisar wucin gadi, wanda zai tabbatar da zartas da sabon daftarin tsarin mulki a majalisar, amma sabo da larabawa na rukunin Sunni suna da fifiko a larduna a kalla dai 4 na tsakiyar Iraki da yammacinta, shugabannin Iraki, ciki har da shugaba Jalal Talabani da shugaban majalisar, Hajem al-Hassani dukansu suna fatan rukunoni daban daban za su gamsu da daftarin tsarin mulkin, ta yadda za a zartas da shi lami lafiya a jefa kuri'ar raba gardama da za a yi a tsakiyar watan Oktoba.
1 2 3
|