A cikin takardar, an kuma bayyana cewa, kasar Sin ta tabbatar da mata da su samu aikin yi daidai kamar yadda maza suke yi a matsayin babban aiki ne da za a yi wajen neman daidaito tsakanin maza da mata da kuma bunkasa harkokin mata, ta kuma dauki wasu matakai a jere. Madam.Gu Xiulian ta ce,'Yawan matan da suke samun aikin yi a kasar Sin ya kai miliyan 337, wato ke nan ya kai kashi kusan 45% na yawan mutanen Sin wadanda suka samun aikin yi.'
A cikin takardar bayanai, an kuma yi bayani a kan matakan da kasar Sin ta dauka a wajen neman tabbatar da hakkin mata a fannonin ba da ilmi da kiwon lafiya da aure da dai sauransu kamar yadda ya kamata.
A cikin shekaru 10 da suka shige, ko da yake an samu babban ci gaba a kasar Sin a fannin neman daidaito tsakanin maza da mata da kuma bunkasa harkokin mata, amma duk da haka, sabo da dalilan bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma, kasar Sin tana ci gaba da fuskantar matsaloli da dama a fuskar neman daidaito tsakanin maza da mata da kuma bunkasa harkokin mata. Sabo da haka, gwamnatin kasar Sin za ta kara aiwatar da manufofi na neman daidaito tsakanin maza da mata, don tabbatar da hakkin mata a fannonin siyasa da tattalin arziki da al'adu da zaman al'umma kamar dai yadda maza suke yi.(Lubabatu Lei) 1 2 3
|