A yau ran 24 ga wata, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta bayar da takardar bayanai dangane da halin da kasar Sin ke ciki a fannin samun daidaito tsakanin jinsuna biyu da kuma bunkasuwar harkokin mata, inda aka yi bayani sosai a kan babban ci gaban da aka samu a kasar Sin a fuskar neman samun daidaito tsakanin jinsuna biyu da kuma bunkasa harkokin mata.
A gun taron matan duniya na hudu na MDD da aka shirya a shekarar 1995 a nan birnin Beijing, an zartas da 'sanarwar Beijing' da kuma 'tsarin ka'idojin aiki', wadanda suka kawo babban tasiri a kan neman samun daidaito tsakanin maza da mata da kuma bunkasa harkokin mata na kasashe daban daban. A yayin da ake tunawa da cikon shekaru 10 da aka kira taron matan duniya na karo na hudu na MDD, kasar Sin ta bayar da wannan takardar bayanai dangane da halin da kasar Sin ke ciki a fannin neman daidaito tsakanin mata da maza da kuma bunkasuwar harkokin mata ne don neman yin cikakken bayani a kan yadda kasar Sin ke neman samun daidaito tsakanin jinsuna biyu da bunkasa harkokin mata a cikin shekaru cikin 10 da suka wuce.
1 2 3
|