
Kasar Mauritania kasa daya ce dake cikin kasashe uku wadanda suka daddale huldar diplomasiya da Isra`ila,amma sojojin da suka yi bore ba su kai hari ga takitin Isra`ila dake Mauritania ba.Jakadan kasar Isra`ila dake wakilci a kasar Mauritania ya riga ya sanar da cewa,`yan diplomasiya na kasar Isra1ila ba su gamu da kurari ba.
An haifi shugaba Taya ne a shekara ta 1941 a kasar Mauratania,ya gama karatu daga makarantar horar da sojojin manyan motocin yaki ta kasar Faransa da jami`ar aikin soja.A watan Disamba na shekara ta 1984,ya hau kan kujerar shugaban kasar Mauritania ta hanyar yin boren aikin soja.A shekara ta 1992,aka zartas da sabon tsarin mulkin kasa,inda aka tanada cewa za a aiwatar da tsarin jam`iyyu da yawa,kuma aka yi zaben shugaban kasa na karo na farko a watan Disamba na wannan shekara,Mr,Taya ya ci nasara a cikin wannan zabe,daga wancen lokaci zuwa yanzu,ya rike mulkin kasar Mauritania a cikin shekaru 21 da suka shige,kuma ya murkushe juyin mulkin soja da aka yi sau tarin yawa.
Bayan da sojojin da suka yi juyin mulkin soja suka sanar da cewa suka tumbuke mulkin Taya,halin da kasar nan ke ciki bai zauna da gindinsa ba,a ran 3 ga wata a kullum sojojin da suka yi juyin mulkin soja suna ta yin tattaunawa domin zaben sabon shugaban kasa,amma ba su sami ra`ayi daya ba tukuna.
Ban da wannan kuma,boren aikin soja ya gamu da zargi daga wajen zaman al`ummar kasashen duniya.Shugaban kawancen kasashen Afirka Alpha Oumar Konare da babban sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Annan sun nuna damuwa kan wannan,kakakin majalisar gudanarwar kasar Amurka Tom Casey ya bayyana cewa,kasar Amurka ta kai suka ga juyin mulkin soja da aka yi a kasar Mauritania,kasar Amurka tana fatan gwamnatin dake karkashin shugabancin shugaba Taya za ta koma kasarta tun da wur wuri haka kuma za ta ci gaba da gudanar da aikinta kamar yadda ya kamata.(Jamila Zhou) 1 2
|