Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-08-05 14:26:12    
An yi juyin mulkin soja a kasar Mauritania

cri

A ran 3 ga wata da asuba,agogon wurin,sojojin rundunar tsaron lafiyar shugaban kasar Mauritania da hukumar tsaron lafiyar kasar sun yi juyin mulkin soja.A wannan rana da yamma,sojojin da suka yi bore sun sanar da cewa,za su kafa kwamitin aikin soja na dimokuradiya da adalci a maimakon ikon mulkin Taya wato Maouya Ould Sid Ahmed Taya.

A ran 3 ga wata da yamma,kwamitin aikin soja na dimokuradiya da adalci ya bayar da wani rahoto ta kamfanin dillancin labarai na Mauritania inda ya bayyana cewa,jama`ar kasar Mauritania sun sha wahala mai tsanani a cikin shekaru gomai da suka shige,gaba daya rundunar sojojin kasar Mauritania da rundunar tsaron lafiyar kasa sun tsai da cewa,za su kawo karshen ikon mulkin Taya.Rahoton ya yi alkawari cewa,kwamitin aikin soja zai kago muhallin dimokuradiya mai adalci ga fannoni daban daban na zaman al`ummar kasar Mauritania,wa`adin rike da mulkin kasa ba zai zarce shekaru biyu ba,haka kuma za a yi aikin share fage da kuma kafa hukumar dimokuradiya ta kasa.Rahoton nan ya bayyana cewa,kwamitin aikin soja zai bi dukkan yarjejeniyoyin duniya da kasar Mauritania ta daddale.

Rundunar sojojin tsaron lafiyar shugaban kasar Mauritania da rundunar sojojin tsaron lafiyar kasar nan sun yi juyin mulkin soja ne yayin da shugaban kasar nan Taya ya je halartar jana`izza na sarkin kasar Saudi Arabiya Fahd Bin Abdul-Aziz.Sojojin da suka yi juyin mulki sun mamaye muhimman sassa daban daban dake hedkwatar kasar nan,alal misali fadar shugaban kasa da gidan redion kasa da fidan redio mai hoto na kasa da ofishin kwanmandan `yan doka na jama`ar kasa da hukumar hafsan hafsoshin kasa da filin jirgin sama da sauransu.Mun sami labari cewa,sojojin da suka yi juyin mulki sun saki shugabannin runkunonin dake yin adawa da su na musulunci da tsohon shugaban yin juyin mulki.Shugaba Taya ba zai iya koma kasar ba,bayan aukuwar boren nan,shugaba Taya ya tashi daga kasar Saudi Arabiya cikin jirgin sama kuma ya isa birnin Niamey na kasar Nijer,shugaban kasar Nijer Mamadou Tanja da jami`an gwamnatin kasar Nijer sun yi masa maraba,shugaba Taya zai zauna a birnin Niamey cikin gajeren lokaci.


1  2