
Bayan kokarin da aka yi wajen tabbatar da shirin tsara birni ta hanyar amfani da albarkatan hallitu masu rai da marasa rai na tattalin arzikin da ake sake yin amfani da shi,muhallin hallitu masu rai da marasa rai na birnin Guiyang ya kara kyautatuwa a bayyane.A cikin `yan shekarun da suka shige,sau tarin yawa an zabi birnin Guiyang da ya zama birnin yawon shakatawa mai nagarta na kasar Sin da birni mai tsabata na kasar Sin.
Kungiyoyin duniya su ma sun darajanta sakamakon da birnin Guiyang ya samu.A watan Maris na shekara ta 2004,hukumar kiyaye muhalli ta majalisar dinkin duniya ta tsai da cewa za ta zabi birnin Guiyang da ya zama sansanin yin gwajin aikin gine-ginen karfin gwamnatin wuri na dauwamammen ci gaban tattalin arziki,kawo yanzu an riga an ware kudin Amurka dala dubu 100 don wannan.Birnin Guiyang shi ma ya sami jari da yawansa ya kai kudin Turai dubu 500 daga kawancen kasashen Turai da jari da yawansa ya kai kudin Turai dubu 200 daga kasar Jamus domin raya tattalin arzikin da ake sake yin amfani da shi.(Jamila) 1 2 3
|