
Bisa bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin cikin saurin gaske,mutanen kasar sun kara mai da hankali kan gine-ginen hallitu masu rai da marasa rai da kiyaye muhalli,sun nuna kwazo da himma don raya tattalin arzikin da ake sake yin amfani da shi ta hanyar yin amfani da kimiyya.
Domin wannan,ana tabbatar da tsarin tattalin arzikin da ake sake yin amfani da shi a birnin Guiyang na lardin Guizhou na kasar Sin.Bisa irin wannan tsari,ba ma kawai za a iya samun dauwamammen ci gaban tattalin arziki ba,har za a iya kiyaye muhallin da muke ciki.
A shekara ta 2002,birnin Guiyang ya tsara babban shiri game da raya tattalin arzikin da ake sake yin amfani da shi,kuma ya tabbatar da dokar birni ta farko ta kasar Sin game da raya tattalin arzikin da ake sake yin amfani da shi a hukunce,ana iya cewa,tattalin arzikin da ake sake yin amfani da shi na birnin Guiyang ya sami yalwatuwa lami lafiya.
1 2 3
|