
Nufinsa na uku shi ne a ran 9 ga watan nan , wato a ranar cikon shekaru biyu da sojojin kasar Amurka suka kai farmaki a birnin Bagadaza , mutanen kasar Iraq sun yi zanga zanga kuma sun nemi sojojin Amurka da su janye jikinsu daga kasar Iraq .
A cikin wannan ziyarar , Mr. Rumsfeld zai sanar wa sababin shugabannin kasar Iraq da matsayin kasar Amurka kan batun janye sojojin kasar.
Nufinsa na hudu shi ne , yanzu halin tsaron da kasar Iraq ke ciki bai kyautatu ba . Dakaru masu dauke da makamai masu adawa da Amurka su kan kai farmaki ga sojojin Amurka dake kasar Iraq. A cikin lokacin ziyararsa , Mr. Rumsfeld zai bukaci shugabannin kasar Iraq da su dauki matakai don kyautata halin da sojojin kasar Amurka ke ciki.
Amma saboda yanzu rukunoni daban daban suna kasancewa da halin adawa da Amerikawa . Wasu kungiyoyi masu makamai sun bayyana cewa , muddin sojojin kasar Amurka suna mamaye kasar Iraq , ba za su daina kai farmaki gare su ba ko daidai da rana daya .
Masu binciken al'amuran duniya sun yi nuni da cewa , matsin lambar da Mr. Rumsfeld ya yi wa sababin shugabannin kasar Iraq a wannan ziyarar ba zato ba tsammani , ko zai sami sakamako ? Ana tantama. (Ado) 1 2
|