
Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labarin cewa , A ran 12 ga watan nan , Donald Rumsfeld , sakataren tsaron kasar Amurka ya kai ziyara a kasar Iraq ba zato ba tsammani. A lokacin ziyarar , Mr. Rumsfeld ya yi shawarwari bi da bi da Jalal Talabani , sabon shugaban kasar Iraq da framinista Ibrahim Jafari . Wannan ne karo na 9 da ya kai ziyara a kasar Iraq bayan da kasar Amurka ta afka wa kasar da yaki.
Masu binciken al'amuran duniya suna ganin cewa , ziyarar da Mr. Rumsfeld ya yi a wannan karo tana da manyan nufofi guda 4.
Nufinsa na farko shi ne yanzu kasar Iraq tana cikin muhimmin lokacin farfado da siyasar kasar . Aikin farfado da siyasar kasar ba kawai ta zama babban matakin zuwa dimokuradiyar Iraq ba , har ma ta kasance da amfanin misali ga gyare-gyaren dimokuradiyar sauran kasashen wannan shiyya . Amma bayan da aka gama babban zabe a ran 30 ga watan Janairu , an riga an yi kusan watanni 3 , har yanzu ba a kafa gwamnatin wucin gadi ba , aikin farfado da siyasar kasar yana tafiyar hawainiya . Saboda haka Mr. Rumsfelda zai matsa wa sababin shugabannin kasar Iraq lamba kuma zai kalubalance su da su kafa sabuwar gwamnati da wur wuri .
Nufinsa na biyu shi ne Iyad Allawi mai kaunar kasar Amurka ya sauka daga mukaminsa kuma Ibrahim Jafari , shugaban Jam'iyyar hadin gwiwar Iraq ya zama firayin ministan rikon kwarya mai cikakken iko , kuma shi ne zai kafa Majalisar ministoci . Wadannan sauye-sauye sun sa kasar Amurka cikin bakin ciki . A ziyarar wannan karo , Mr. Rumsfeld zai shawo kan Mr. Jafari da ya kiyaye daidaici tsakanin rukunoni daban daban kan matsalar kafa majalisar ministoci .
1 2
|