
Bayan da kasashen Turai suka kara kyautata manufofinsu cikin rabin karnin da ya shige, hakikanin karfinsu yana nan yana kara karfafuwa, wato a duniyar yau, sun zama wani muhimmin karfi.
Yake yaken da aka yi a kasar Iraq sun kawo sauye sauyen dangantakar dake tsakanin kasar Amurka da kasashe musulmi. Yawacin kasashen musulmi sun nuna kiyewarsu ga yake yaken da kasar Amurka ta tayar ga kasar Iraq, Kuma kasar Amurka tana son mai da kasar Iraq da ta zama misalin koyo ga sauran kasashen dake shiyyar Gabas ta tsakiya, An aza harsashi ga kasar Amurka wadda za ta tafiyar da dimakuradiyya iri ta kasar Amurka a shiyyar Gabas ta tsakiya, wannan ya jawo damuwar kasashen musulmi na shiyyar gabas ta tsakiya. Ban da haka kuma yakin da aka yi a kasar Iraq ya jawo kiyewar da musulmi na duk duniya suka nuna wa kasar Amurka.
A karshe dai an bayyana cewa, kafin kasar Amurka ta tayar wa kasar Iraq farmaki, kasar Amurka ta taba yin amfani da majalisar dinkin duniya wajen tafiyar da manufarta. Amma bayan yakin kasar Iraq, sai kiri da muzu ne wadansu kwararru da masana na kasar Amurka sun yi kirkiro cewa, za a kafa kawancen kasashen dimakuradiyya don maimakon majalisar dinkin duniya.(Dije) 1 2
|