 Kafin shekaru biyu da suka shige,kiri da muzu ne kasar Amurka ba ta kula da ra'ayin majalisar dinkin duniya ba sai ta tayar wa kasar Iraq yake yake, har an jawo babban rikici ga kasashen duniya tun bayan yakin sanyi. Har wa yau dai irin barnar da aka kawo daga yake yake ba ta rushe kwata kwata ba.
Kuma irin tasirin da aka kawo wa dangantakar dake tsakanin kasashen duniya da dokokin shari'a na duniya yana nan yana kara bayanuwa a fili.
Da farko dai, yakin kasar Iraq ya kawo wani misalin cewa, daga wani gefe na waje an canja halin mulkin kasa mai mallakar kai tare da karfin makamai. A shekara ta 2002, kasar Amurka ta bayar da wani" rahoton kiyaye kwanciyar hankali na kasa", a cikin wannan rahoto, kasar Amurka ta gabatar da dabarar yaki wai kai farmaki a gaban, Kana kuma a cikin yake yaken kasar Iraq ne ta fara yin amfani da wannan dabarar yaki. Bisa wannan aron baki ne kasar Amurka ta iya tayar wa kowace kasa farmaki bisa ra'ayinta kawai. Ba shakka, wannan zai iya jawo barazana da yamutsatsen hali ga kasashen duniya.Cikin 'yan shekaru biyu da suka shige, mutane suna iya gani cewa, sakamakon da aka kawo daga yake yaken kasar Iraq shi ne wadansu kasashen duniya suna nan suna kara jin tsoro. Sai sun shiga sabuwar gasar jan damara, har ana neman sayo manyan makamai masu kare dangi.
Cibiyar ka'idojin dangantakar dake tsakanin kasashen duniya tana girmama wa mallakar kai da cikakken yankin kasa da rashin kai wa juna hari da rashin yin shishigi ga harkokin gida na sauran kasashe.
Ban da haka kuma, yake yaken kasar Iraq ya jawo sauye sauyen dangantakar dake tsakanin kasar Amurka da kasashen Turai, har an sa dangantakar dake tsakanin gabobi biyu na tekun Atlantic ta kara zafi sosai. Masana na kasashen Turai suna gani cewa, daga yake yaken nan ne kasashen Turai suna kara gane manufar sabuwar daulantaka ta kasar Amurka. Kuma kasar Amurka ta banbanta kasashen da suka nuna goyon baya ko ba haka ba ga manufarta ta tayar wa kasar Iraq yake yake, wannan ya kara jawo sabani tsakanin kasashen Turai.
1 2
|