An bayyana cewa, abinci iri 5 su ne rukuni na farko da kasar Sin ta aiwatar da tsarin ba da takardar izinin shiga kasuwanni. Amma cikin shekarar 2001, hukumomin kasar Sin da al'amarin nan ya shafa sun yi bincike sosai cikin duk kasa kan kamfanonin sarrafawa, an gano cewa, da akwai kamfanoni wajen dubu 60 da ke sarrafa abinci iri 5, yawan ingancinsu da ke dacewa da gwamnatin kasar Sin ta kayadde bai kai kashi 60 cikin dari ba. Ya zuwa ran 1 ga watan Fabarairu na shekarar 2004, wato lokacin da akea aiwatar da tsarin ba da izinin shiga kasuwanni, kamfanoni dubu 6, rabinsu sun sami takardar, sai aka tankade sauransu .
Jami'ai na hukumomin da al'amarin nan ya shafa na kasar Sin sun fayyace cewa, kafin ran 1 ga watan Yuli na bana, za a kammala aikin sa ido da ba da takardar izinin. Bayan ran 1 ga watan Yuli, duk kayayyakan da ba su sami takardar izinin sarrafawa ba, ba za a sami damar sayar da su cikin kasuwanni ba.
Bisa shirin da aka yi, cikin shekaru masu zuwa, kasar Sin za ta aiwatar da tsarin ba da takardar izinin sarrafawa ga duk abinci. Kuma kasar Sin ta kasa abinci da su zama iri 28, da akwai iri 13 da basu sami takardar izinin ba tukuna, yanzu an soma aikin bada takardar izinin shiga kasuwanni tun ran 1 ga watan Janairu na 2005. Kafin a soma aikin nan, hukumomin da al'amarin nan ya shafa sun yi aikin bincike kan sharuda da suka wajaba na kamfanoni, har an rubuta takardun tarihi na ingancin abinci iri 13, wato na kamfanoni masu yawan dubu 19. An tsara babi filla-filla na shigar da abinci iri 13 cikin kasuwanni, yanzu hukumomi na wurare daban dabam suna karbar bukatun da kamfanoni suka gabatar, suna yin aikin sa ido da ba da takardar izinin shigar da abinci cikin kasuwanni.(ASB) 1 2
|