Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-02-21 16:46:36    
Kasar Sin ta kara sa ido kan ingancin abinci

cri
Domin kyautata ayyukan kamfanonin sarrafa abinci da daga matsayin ingancinsu, tun daga watan Augusta na shekarar 2002, kasar Sin ta aiwatar da wani tsarin ba da izinin shigar da abinci cikin kasuwanni. Bisa tsarin nan, wajibi ne duk kamfanonin sarrafa abinci su gabatar da rokonsu ga hukumomin gwamnatin da al'amarin nan ya shafa wajen sayar da abincinsu, in an yarda bayan da aka sa ido, sai abincin da kamfanin nan ya sarrafa zai sami wata takardar sarrafa shi, abincin da ya sami takardar sarrafa shi, za a iya sayar da shi cikin kasuwanni.

Amma takardar sarrafawa ba na dindindin ba ne. Lokacin da aka gano matsalar ingancin abinci cikin sa ido da akan yi , to za a yanke hukunci kan kamfanin, har ma za a soke takardar sarrafawa da ya samu.

Tun bayan da aka soma aiwatar da tsarin ba da izinin shigar da abinci cikin kasuwanni, ana yunkurad da ayyuka da al'amarin nan ya shafa taki kan taki. Daga ciki, an kammala aikin ba da takardar izini ga shinkafa da garin alkama da man girki da ruwan magin waken soya da ruwan tsami guda 5 , bayan haka matsayin ingancin abonci iri 5 nan ya dagu a bayyane.

A shekarar 2004, ingancin abincin da suka sami takardar izinin shiga kasuwanni duk ya karu. Ciki an duba abinci iri 5 wato shinkafa da garin alkama da man girki da ruwan magin waken soya da ruwan tsami, wajen kashi 91.4 cikin dari sun kai matsayin da aka kayadde, wanda ke nan ya karu da kashi 31.5 cikin dari bisa na shekarar 2001, wato kafin aiwatar da tsarin bada takardar izinin shiga kasuwanci.


1  2