|
Yayin da yake takalo magana kan matsala game da ko sakamakon babban zaben da za a samu zai jawo yakin basasa a kasar Iraki,shehu malami Yin Gang wanda ya zo ne daga ofishin yin nazari kan harkokin yammancin Asiya da Afirka na cibiyar yin nazari kan ilmin kimiyya da zaman al`umma ta kasar Sin yana ganin cewa,irin wannan hali ba zai faru ba.Ya ce,`Daga ayyukan share fage da jam`iyyu daban daban na kasar Iraki suka yi,ana iya cewa,ko shakka babu yakin basasa ba zai auku ba.A akasin haka,zaman al`ummar kasar Iraki zai sami kyautatuwa a kai a kai a nan gaba.`
Kodayake kasar Amurka ta kawo tasiri ga babban zaben saboda sojojin kasar Amurka da yawansu ya kai dubu 150 suna zaune a kasar Iraki,amma shehu malamai Li Shaoxian ya yi nuni da cewa,majalisar dinkin duniya da gwamnatin wucin gadi ta kasar Iraki sun shugabanci wannan babban zabe.
Kafofin watsa labarai suna ganin cewa,kamata ya yi kasar Amurka ta janye jiki daga kasar Iraki tun da wur wuri.Kan wannan kuma,tsohon jakadan kasar Sin dake wakilci a kasar Iraki Sun Bigan ya dauka cewa,kasar Amurka ba za ta janye jiki daga kasar Iraki ba kafin ta sami moriyar tsare-tsare da tattalin arzikin da take bukatar.(Jamila Zhou) 1 2
|