Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-02-01 09:09:53    
Masanan kasar Sin kan matsalar Gabas ta tsakiya sun yi sharhi kan babban zaben Iraki

cri

A ran 30 ga wata,an kawo karshen babban zaben kasar Iraki,a halin da ake ciki yanzu,ana yin kididdigar yawan kuri`un da aka jefa.Kodayake al`amuran kai hari masu nuna karfin tuwo a jere sun faru a wurare daban daban yayin da ake jefa kuri`a,amma kashi 60 cikin dari na masu jefa kuri`a sun shiga babban zaben,wannan ya zarce kimmantawar mutane.Za a sami sakamako bayan kwanaki goma,amma wasu labarai game da babban zaben sun jawo hankulanmu.Wasu masanan kasar Sin kan matsalar Gabas ta tsakiya sun yi sharhi kan wannan.

Shehu malami na cibiyar yin nazari kan huldar dake tsakanin kasa da kasa na zamanin yau na kasar Sin Li Shaoxian yana ganin cewa,ana iya cewar,an tafiyar da babban zaben lami laifya.Ya ce,`An kammala babban zaben kasar Iraki lami lafiya,wannan ya zarce kimmantawarmu.Da farko dai,ba a gamu da babbar wahala a fannin kwanciyar hankali ba,na biyu,masu jefa kuri`a sun yi yawan gaske,a kalla dai sun kai kashi 60 cikin dari.Duk wadannan sun shaida mana cewa,mutanen kasar Iraki suna fatan za su yin zaman rayuwa kamar yadda ya kamata,kuma rukunin Shiite da rukunin Kurd sun nuna kwazo da himma kan babban zaben.Ban da wannan kuma,kashin masu jefa kuri`a na rukunin Sunni ba shi da yawa ba,amma bai yi kasa kasa ba.`

Kan tasirin da wannan babban zabe zai kawo wa tsarin siyasa na kasar Iraki a nan gaba,shehu malami Li Shaoxian yana ganin cewa,wata kila babban zaben zai sa nufin baraka na Iraki ya kara tsanani.Ya ce,`Daga halin jefa kuri`a,ana iya ganin cewa,a kan siyasa,rukunin Shiite zai ba da jagora,jam`iyyu biyu na rukunin shiite wato kawancen hada kan Iraki da kungiyar hadin gwiwar Iraki za su sami matsayi mai rinjaye a cikin majalisar dokoki mai wucin gadi ta kasar Iraki a nan gaba.Ban da wannan kuma,matsayin mutanen rukunin Kurd zai kara karfafuwa.Kazalika,wasu jam`iyyun rukunin Sunni sun nuna kiyayya ga babban zaben.Duk wadannan za su sa nufin kawo baraka na kasar Iraki ya kara tsanani.Yanzu abu mafi muhimmanci shi ne yaya za a hada kan Iraki.


1  2