Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-01-19 11:29:02    
Ya kamata Iraq ta kara karfin sojojinta na tsaro

cri

Kayan aiki na sojoji 'yan sanda na Iraq ba su da kyau idan an kwatanta da na sojojin Amurka a Iraq.A kan titunan birnin Bagadaza,ka kan ga sojojin Amurka cikin motoci tare da hular kwano a kai.Amma sojoji 'yan sanda na Iraq,lorori ne ke dauke da su,ba su rigunan da suka kare kansu daga harsasai,mayani ne a kan rufe fuskokinsu kawai.Ministan harkokin gida na Iraq ya ce tun tashin yakin Iraq a shekara ta 2003,'Yan sanda kimanin dubu uku sun mutu saboda hare hare da dakaru masu adawa da Amurka suka kai musu.Wannan adadi ya fi na sojojin Amurka yawa da ninki biyu ko fiye.

Yayin da ranar zaben gama gari na Iraq za ta kusanto,a gnin Amurka da gwamnatin rikon kwarya ta Iraq,rundunar sojan tsaron kasa ta kasar Iraq ba ta iya cika dawainiyyar tabbatar da tsaron kasa ba.A ranar bikin krismati na shekarar bara,sakataren tsaron kasar Amurka Mansfield ya bayyana cewa za a kara yawan sojojin Amurka a Iraq daga dubu 138 zuwa dubu 150 domin tabbatar da tsaron zabe.A birnin Bagadaza,babban birni na kasar Iraq wanda ya fi muhimmanci a zabe,an kara sojojin Amurka dubu biyar da yawansu ya kai dubu 34.A birnin Mosul dake arewancin kasar Iraq, Amurka tana nan tana aiwatar da shirin kara yawan sojojinta

Bisa labarin da aka samo daga Amurka,an ce babban kwamandan sojojin Amurka a Iraq yana nan yana nazarin wata shawara game da tura mashawartan soja na Amurka zuwa kasar Iraq.Bisa wannan shawarar da aka kawo,wadannan mashawartan soja na Amurka za su shiga ayyukan ba da horo ga sojojin tsaro na kasar Iraq.Wani rahoton wani jami'in ma'aikatar tsaron kasa ta Iraq ya rubuta a karshen rabin shekarar bara ya yi nuni da cewa,za a kammala ayyukan ba da horo ga sojojin tsaron kasa na Iraq a watan Yuni na shekara ta 2006.

Kan halin da sojojin tsaron kasa na Iraq ke ciki,babban mashawarcin soja na ma'aikatar tsaron kasa ta Iraq janar mai taurari hudu Gabari ba da dadewa ba ya ce lokaci bai yi ba da sojojin tsaron kasa na Iraq na daukar nauyin kare doka da oda a kasar Iraq.(Ali)


1  2