Bayan da aka hamburar da gwamnatin Saddam Hussein,rundunar soja da ma'aikatun lekon asiri dukkansu sun wargaza.Ga shi a yau Iraq tana da wata rundunar sojojin tsaron kasa da yawan sojojinta ya kai dubu 130.Duk da haka kamata ya yi Iraq ta kara karfin sojojinta na tsaro wajen tafiyar da harkokinta.
Wasu tsauraran matakan da sojojin Amurka suka dauka bayan mamayensu a Iraq sun haddasa dakaru masu adawa da Amurka habaka.Kan matakin da sojojin Amurka a Iraq suka dauka,dakaru masu adawa da Amurka su kan mayar da martani,har ma Amurka ta yi mamaki da ganin karfin da dakaru masu adawa da Amurka ke da shi.Duk da haka cigaban rundunar tsaron kasa ta Iraq bai iya biyan bukatun da ke akwai a yanzu ba.
A shekarar bara yayin da sojojin Amurka a Iraq da sojojin tsaron kasa na Iraqsuka kai hare hare kan "sojojin mahdi" na Sadr.Sama da kashi hamsin cikin kashi dari na sojojin tsaron kasar Iraq sun tsere.A larduna dake da rikice rikice a kasar Iraq,sojojin tsaron kasa da suka tsere sai kara yawa suke,babu isasun kwamandoji sojoji ma ba su kware a fagagen yaki.Rawar da wannan rundunar ta taka a yanzu ta bayyana cewa ba su da shiri sosai na tabbatar da harkokin tsaro a kasar Iraq idan sojojin Amurka za su mika su.
Da yawa daga Sojojin tsaron kasa na Iraq sun yi aiki ne domin samu kudi.A kasar Iraq kusan kashi hamsin cikin kashi dari na mutanen Iraq ba su da aikin yi,wani sabon dan sanda na Iraq ya iya samun albashi na dalar Amirka kimanin 250 amma a lokacin mulkin Saddam dalar Amurka 15 gare shi.Shi ya sa mutane da yawa sun shiga rundunar soja ne domin samu kudi da iyalinsa,wannan abu ba ya amfana wa rundunar sojan tsaro ta kasar Iraq ba.
1 2
|